Ga yadda sojojin kasar Sin suke tsaron yankunan dake kan iyakar wucin gadi dake tsakanin kasashen Lebanon
2021-02-08 09:00:00 CRI
Ga yadda sojojin kasar Sin masu tabbatar da zaman lafiya a kasar Lebanon a madadin MDD suke tsaron yankunan dake kan iyakar wucin gadi dake tsakanin kasashen Lebanon, da Isra’ila a ran 3 ga watan Faburairun da muke ciki. An yi amfani da ganguna masu launin shudi, an kafa wannan layi mai tsawon kilomita 121 dake kan iyakar wucin gadi dake tsakanin kasashen Lebanon da Isra’ila. Sakamakon haka, an kira shi layi mai launin shudi. (Sanusi Chen)