logo

HAUSA

Murnar bikin bazara a wurin aiki ya fi tsaro yayin kandagarkin COVID-19

2021-02-05 19:05:27 CRI

Murnar bikin bazara a wurin aiki ya fi tsaro yayin kandagarkin COVID-19_fororder_1

Bikin bazara, biki ne mafi girma cikin jerin bukukuwan gargajiyar kasar Sin, wanda ke da dogon tarihin da ya kai shekaru sama da dubu hudu, a don haka, bisa al’adar gargajiyar kasar, ya dace Sinawa su fara shirye-shiryen komawa gida domin saduwa da iyalai, amma yanzu miliyoyin Sinawa su hakura da komawa gida, domin kaucewa kara barkewar annobar COVID-19 da yanzu haka wasu kasashen duniya suke shan fama da ita, inda za su yi bikin a wuraren da suke aiki.

A bana bikin bazara ya fado ne a ranar 12 ga watan Fabarairu, shin yaya Sinawa suke murnar wannan gagarumin bikin bazara na musamman a wannan yanayin da ake ciki na kandagarkin cutar?

Domin kara karfafa gwiwar al’ummar kasar yayin da suke taya murnar bikin bazara a wuraren aiki, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wasu manufofi a kokarin da ake na ba da karin damammakin sayen kayayyaki yayin bikin, alal misali, kafofin sayar da kayayyaki ta yanar gizo daban daban na kasar Sin, sun shirya bikin sayar da kayayyaki na shekarar 2021 cikin hadin gwiwa karkashin jagorancin ma’aikatar kasuwancin kasar tun daga karshen watan Janairun da ya gabata.

Alkaluman binciken da aka fitar sun nuna cewa, Sinawa, musamman ma matasa, sun fi son sayen kayayyaki ta yanar gizo domin aikewa gida, ta wannan hanya ne suke bayyana fatan alheri na sabuwar shekara ga iyalansu.

Wasu matasa sun fi son sayen kananan kayayyakin laturoni da ake amfani da su a cikin gida ga iyayensu, domin kyautata rayuwarsu ta hanyar rage aikin gida, alkaluman dandalin sayar da kayayyaki ta yanar gizo na Suning sun nuna cewa, wadannan kayayyakin sun hada da tukunyar dafa abinci da kanka dake amfani da lantarki, da tanda, da tukunyar soya abinci ba tare da yin amfani da man girki ba, kuma alkaluman dandalin sayar da kayayyaki ta yanar gizo na TMALL sun nuna cewa, yayin bikin, na’urar yin taliya, da na’urar tsabtace kasa, da na’urar wanke tasa sun fi samun karbuwa.

Kana dandalin JD shi ma ya fitar da alkaluma dake nuna cewa, matasa da dama sun fi son sayen abinci mai gina jiki ga iyayensu da kakanninsu, har adadin abincin da aka sayar da su a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ya karu da kaso 69 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Hakazalika, kayayyakin da aka samar ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, kamar su kayan dumama abinci, da tukunyar dafa abin sha mai gina jiki da ake sarrafawa da murya da sauransu sun fi samun kaubuwa a wajen matasan kasar, wadanda aka haife su bayan shekarar 1990 ko shekara ta 2000.

A bayyane an lura cewa, Sinawa suna jin dadi matuka ta hanyar murnar bikin bazara a wurin aiki, hakan shi ma zai taimaka wajen tabbatar da lafiyar jama’a a yayin da ake kandagarkin annobar COVID-19.(Jamila)

jamila