logo

HAUSA

Ba dukkan kasashe masu karfi ne suke son nuna danniya ko babakere ba, in ji Xi Jinping game da neman ci gaban kasar Sin cikin lumana

2021-01-29 15:03:25 CRI

A ranar 28 ga watan Janairun 2013, jim kadan bayan da ofishin siyasa na kwamitin koli na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kama aiki, ya gudanar da taro game da batun "Tsayawa kan hanyar neman ci gaba cikin lumana". A yayin da shugaban kasar Xi Jinping ke shugabantar taron, ya tabbatar da cewa, ya zama dole "a karfafa tushen bin hanyar samun ci gaba cikin lumana." Tun daga wannan lokaci, Xi Jinping ya bayyana manufar samun ci gaban kasar Sin cikin lumana ga duniya a lokuta da dama. Bin hanyar samun ci gaba cikin lumana ya zama jigon tunanin diflomasiyyar Xi Jinping.

“Ta yaya kasar Sin ke bunkasa? Wace irin kasa ce Sin zata zama bayan ci gaba? Akwai ra'ayoyi mabanbanta a tsakanin kasashen duniya game da wadannan batutuwan biyu. Wasu sun tabbatar da kasar Sin sosai, wasu suna cike da imani kan kasar Sin, wasu suna damuwa da kasar Sin, wasu kuma a ko da yaushe ba sa farin ciki da kasar Sin. A gani na, wannan ba abin mamaki ba ne, kasar Sin babbar kasa ce mai yawan al’umma sama da biliyan 1.3, ta zama tamkar wani katon mutum a tsakanin mutane. Ko shakka babu, saura jama’a suna sha’awar ganin yadda wannan mutum mai girma ke tafiya da motsawa, ko zai yi karo da su, ko kuma zai toshe hanyarsu, ko kuma zai mamaye yankinsu.”

Shugaba Xi Jinping ya bayyana haka ne a yayin jawabinsa a zauren majalisar dokokin tarayyar Australia a ranar 17 ga Nuwamban 2014, inda ya yi amfani da "katon mutum" don bayyana halin da kasar Sin ke ciki don tinkarar shakkun da kasashen duniya suke nunawa kasar Sin a wancan lokacin. Xi Jinping ya jaddada cewa, jama'ar kasar Sin suna bin hanyar ci gaba cikin lumana, yana fatan dukkan kasashen duniya za su bi wannan hanya ta samun ci gaba cikin lumana, domin hada kai wajen magance kalubalolin da ke kawo cikas ga zaman lafiya, tare da hada hannu don gina wata duniya mai dorewar zaman lafiya da samun wadata tare.

A hakika dai, wannan ba shi ne karo na farko da Xi Jinping ke yin irin wannan bayani ga kasashen ketare ba. Yayin da kasar Sin ta kai matsayi na biyu a fannin karfin tattalin arziki a duniya, wasu mutane sun fara nuna damuwa game da ko wannan "katon mutum" mai tasowa zai kama  hanyar nuna danniya ko babakere sakamakon karfin da ta samu .

A ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2014, a wajen asusun Kolber da ke kasar Jamus, Xi Jinping ya gabatar da jawabi bisa taken tsayawa kan hanyar samun ci gaba cikin lumana da kasarsa ke yi, inda ya yi bayani sosai kan hanyar ci gaban kasar Sin, don taimakawa sassa daban daban na duniya wajen kara fahimtar kasar Sin. Xi Jinping ya ce,

“Kasar Sin kasa ce mai son zaman lafiya. Kasar Sin na bukatar zaman lafiya, kamar yadda mutane ke bukatar iska, kuma kamar yadda komai ke bukatar hasken rana don girma. Kasar Sin ba ta yarda da cewa, idan wata kasa ta samu karfi, dole sai ta kasance mai nuna fin karfi ba. A cikin duniyar yau, ko tsohuwar hanyar mulkin mallaka da fin karfi za ta iya ci gaba da aiki ko a’a? Amsar ita ce a’a. Ba wai kawai ba za su iya ci gaba da aiki ba ne, har ma tabbas za a kawar da su. Sai dai hanyar ci gaba cikin lumana ce kawai zata iya aiki. Saboda haka, kasar Sin za ta nace ga bin hanyar samun ci gaba cikin lumana.”

Duniya a yau tana fuskantar manyan sauye-sauye wadanda ba a taba ganin irinsu ba a karni daya da ya wuce, ra’ayin bangaranci, da na ba da kariya, da kuma ra’ayin nuna danniya na yunkurin tasowa a halin yanzu. Me ke faruwa a duniya, yaya za mu yi? A ganin Xi Jinping, duniya ita ce duniyar jama’a na dukkan kasashe, don haka matsaloli da kalubalolin da duniya ke fuskanta na bukatar jama’ar dukkan kasashe su taimaka wa juna tare da hada kai don magance su tare. Neman ci gaba cikin lumana da cimma nasara tare ta hanyar hadin kai ita ce hanya madaidaiciya a duniya. Xi Jinping ya ce,

“A matsayinta na babbar kasa mai daukar nauyi, kasar Sin na rungumar kyawawan dabi'un dukkan bil'adama na zaman lafiya, ci gaba, adalci, dimokuradiyya, da 'yanci, tana kuma bin ra'ayin gudanar da harkokin duniya ta hanyar yin shawarwari da juna, da kuma more nasarorin da aka cimma tare. Kana tana tsayawa kan hanyar neman ci gaba tare cikin lumana da bude kofa ga juna da hada kan juna. Muddin muka tsaya kan hanyar ci gaba cikin lumana, da yin kokari tare da jama’ar kasashe daban daban don raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkanin ‘yan Adam, tabbas za mu iya tabbatar da makoma mai kyau irin ta zaman lafiya da bunkasuwa.” (Bilkisu)