logo

HAUSA

Ya kamata kasashen duniya su gudu tare, don su tsira tare

2021-01-26 16:15:09 CRI

Yayin taron dandalin tattauna harkokin tattalin arzikin duniya da aka fara jiya Litinin, wanda ya hada shugabannin duniya don tattauna hanyoyin tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi, wanda ya fadakar da kasashen duniya tare da bada kwarin.

Cikin jawabin, shugaba Xi Jinping, ya ce babu tantama za a cimma nasarar yaki da cutar COVID-19, ya kuma nanata wajibcin ci gaba da yakar cutar. Wannan zai ba kasashe da al’umma kwarin gwiwar yaki da cutar, la’akari da cewa, a farkon bullarta, Sin ta fi kowace kasa fama da ita, amma a yanzu, ita ce kasar da ta fi kowace cin galaba a kanta. Lallai nasarorin da Sin ta samu, za su bada kwarin gwiwa ga kasashe da al’ummomi wajen yin abun da ya dace domin ganin bayan cutar.

Xi Jinping ya kara da cewa tsari da yanayin kowace kasa sun sha bamban, a don haka ya yi gargadi game da tilasta wani matsayi kan tsarin zamantakewar wasu. Hakika dukkan bil Adama na da matsayin iri daya, wato babu wanda ya fi wani, sannan makomarsu na hade da juna. Yadda halin kowane mutum ya bambanta, haka ma na kasashe, ya kamata kowace kasa ta gano yanayin da ya fi dacewa na samun ci gaba. Sannan bai kamata wata kasa ta ce za ta kakaba akidunta kan wasu ba. Muddun ana son duniya ta ci gaba cikin zaman lafiya da lumana, to dole ne a girmama bambance-bambancen dake akwai tsakanin kasa da kasa. Kamar yadda shugaban ya bayyana, “Kasashe na da ’yancin zabin kasancewa tare ta hanyar mutunta juna yayin warware bambance-bambance, da yayata musaya da koyi da juna”.

Shugaban na Sin ya kuma tabo batun taimakawa kasashe masu tasowa da samar da damarmaki da dokoki ta yadda kowa zai amfana. Wannan muhimmin lokaci da ake ciki, ya kara nunawa duniya bukatar taimakekeniya a tsakanin kasashe, musamman masu karfi zuwa ga kanana. Ci gaban wata kasa ba zai taba dakushe ci gaban wata ba. Ya kamata dukkan wasu damarmaki da dokokin da za a bullo da su a matakin kasa da kasa, su amfanawa dukkan kasashe ba wasu tsiraru ba. Ci gaban kasashe masu tasowa, zai taka muhimmiyar rawa wajen rage tarin matsalolin da ake fuskanta a duniya.

Babu wata kasa guda da za ta iya magance matsalar da duniya ke fuskanta. Wajibi ne kasashen duniya su hada kai, su dauki mataki tare. Kamar yadda kullum kasar Sin ke kira da huldar kasa da kasa, dole ne a hada gwiwa ta hanyar gabatar da mabanbantan dabarun tunkarar matsalolin da bil adama da duniya ke fuskanta domin a gudu tare a tsira tare. (Fa’iza Mustapha)