Mazauna birnin Shigatse na murna shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyarsu
2021-01-21 14:53:21 CRI
A birnin Shigatse na jihar Xizang ta kasar Sin, al’umma na murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya na kabilar Zang. Ana daukar birnin na Shigatse a matsayin ma’adanar abinci ta jihar Xizang a sakamakon yadda ayyukan gona suka ci gaba sosai a wurin. A zamanin da, mazauna wurin su kan yi bikin murnar shiga sabuwar shekara a wata na 12 bisa kalandar gargajiyarsu, wato wata guda kafin sauran sassan jihar Xizang suka fara shagulgula, ta yadda za su ji dadin bikin ba tare da bata aikin gona ba.(Lubabatu)