logo

HAUSA

Sin ta jawo jarin waje na kimanin Yuan triliyan 1 a shekarar 2020

2021-01-21 15:27:00 CRI

Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fitar da rahoto a jiya Laraba, wanda ya nuna cewa, a cikin shekarar 2020 da ta shude, kasar ta yi kokarin dakile cutar COVID-19 tare da samun nasarori, yawan jarin wajen da ta yi amfani da shi ya karu, duk da cewa yawan jarin da kasashe daban daban ke zubawa a ragowar kasashe ya ragu matuka. Alkaluma sun bayyana cewa, yawan jarin wajen da Sin ta jawo a duniya ya karu matuka. Abin da ya nuna cewa, Sin tana ba da tabbaci da samar da mafita ga aikin zuba jari na kasashe daban daban.

Alkaluma na nuna cewa, a cikin shekarar 2020, yawan jarin waje da Sin ta yi amfani da shi a bangaren da bai shafi hada-hadar kudi ba, ya kai Yuan biliyan 999.98 wanda ya karu da kashi 6.2%, adadin da ya kai sabon matsayi a tarihi. Shugaban sashin jarin waje na ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Zong Changqing ya shedawa manema labarai cewa, Sin ta kyautata tsarinta na shigo da jarin waje, kuma ta tabbatar da wuraren da ta shigo da jari, ya ce:

“Sana’o’in ba da hidima sun samu yin amfani da jarin waje da yawansa ya kai Yuan biliyan 776.77, wanda ya karu da kashi 13.9%,  tare da kasancewa kashi 77.7% na dukkanin jarin waje da ake amfani da shi. Ban da wannan kuma, yawan jarin da sha’anin kimiya da fasaha ya janyo ya karu da kashi 11.4%, wannan adadi a fannin ba da hidima ta fuskar kimiyar zamani ya kai 28%. Haka kuma Sin ta samu tabbatar da wuraren da take jawo jarin waje. Yawan jarin da kasashe 15 da suke sahun gaba wajen zuba jari a kasar Sin suka zuba, ya karu da 6.4%, daga cikinsu Holland da Birtaniya sun samu karuwar kashi 47.6% da 30.7%, wannan adadi a kungiyar ASEAN ya kai 0.7%. ”

Yawan jarin wajen da Sin ta jawo daga ketare ya samu karuwa, duk da cewa cutar COVID-19 ta raunana tattalin arzikin duniya sosai. A cewar Zong, karuwar tattalin arzikin kasar Sin na da alaka da tsare-tsaren da Sin take dauka, wato dakile cutar COVID-19 cikin lokaci, da ba da tabbaci ga komawa bakin aiki, da ingiza bunkasuwar kamfanoni. Ban da wannan kuma, Sin ta aiwatar da jerin manufofi don tabbatar da shigo da jarin waje. Ya ce:

“Sin ta yi wa jerin sunayen sana’o’i da ayyukan da aka haramta kamfanonin kasashen waje zuba jari gyara har sau 6 cikin shekaru bakwai. Inda ta yiwa takardar jerin sana’o’i da ayyukan da ake zuba jari kansu gyara cikin shekaru 2 a jere.Alkaluman da ma’aikatar kasuwanci ta fitar sun nuna cewa, kaso 60 cikin 100 na kamfanoni masu jarin waje dake nan kasar Sin sun samu karuwar riba, kuma kimanin kashi 90% sun yi amanna kan makomarsu.”

Ban da wannan kuma, yayin da aka shiga lokaci mafi wahala wajen dakile cutar COVID-19, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yi kokarin warware matsalolin da kamfanoni masu jarin waje suka fuskanta na karancin kayayyakin kandagarki da wahalar samun iznin wuce kwastam da kayayyaki, da matsalar komawa bakin aiki, inda ta ba da taimako ga ma’aikatan kasashen waje dubu 16 don su shiga kasar Sin. A sa’i daya kuma, a wasu lardunan da suka fi jawo jarin waje, ma’aikatar ta kafa tsarin ba da tabbaci. Zong ya ce, wasu manyan kamfanoni dake da rassa daban-daban a duniya sun kara zuba jari a kasar Sin, ciki hadda Exxon Mobil da Daimler AG da BMW da Toyota da LG da sauransu.

Abin lura shi ne, Sin ta kafa sabbin yankunan ciniki cikin ‘yanci 3 a Beijing da Hunan da Anhui, tare da habaka irin wannan yankin a Zhejiang, da gabatar da shirin kafa tashar ciniki cikin ‘yanci a Hainan. Alkaluman da aka fitar a shekarar 2020 sun nuna cewa, yawan jarin wajen da yankunan gwajin ciniki cikin ‘yanci 21 suka jawo ya kai kashi 17.9% cikin dukkan jarin da aka zuba a kasar Sin.

Ya zuwa yanzu, yawan kamfanoni masu jarin waje ya kai kashi 2% na dukkanin kamfanoni dake Sin, wadanda suka samar da guraben aikin yi da ya kai kashi 10% a birane, da biyan haraji na kashi 1/6 da ma ayyukan shigi da fici na kashi 2/5. Game da hakan, Zong ya ce, jarin waje na taka rawa sosai wajen daga matsayin tattalin arziki da karfin kimiya da fasaha da karfin kasar da ma zamantakewar al’umma, bisa karfin kasuwannin cikin gida da waje. Saboda haka, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin za ta ci gaba da jawo jarin waje tare da kara bude kofar kasar ga ketare don jawo karin jari daga kasashen waje. Ya ce:

“Sin za ta ci gaba da yin kirkire-kirkire kan jerin sana’o’i masu jawo jarin waje don ingiza dunkulewar sana’o’i daban-daban tsakanin Sin da waje, da ci gaba da gaggauta bude kofa ga waje, da ma kyautata tsarin ba da tabbaci ga jarin waje, da zurfafa kwaskwarima kan manufofin jawo jarin waje, ta yadda za a samar da wani yanayi mai armashi a fannin jawo jarin waje.” (Amina Xu)