logo

HAUSA

Amurka ta kasa magance matsalar rashin daidaito a cikin al’ummarta

2021-01-20 13:44:11 CRI

 

Amurka ta kasa magance matsalar rashin daidaito a cikin al’ummarta_fororder_微信图片_20210120134154

Sakamakon bazuwar cutar COVID-19, wadda ta raunana tattalin arzikin duniya sosai, yanzu a kasar Amurka, gibin da ke akwai tsakanin al’ummar kasar ta fuskar mallakar dukiyoyi na kara yawaita.

Fareeha Haq, wata ‘yar kasar Amurka ce wadda ta taba aiki a wani sashen raba tallafin abinci ga mutanen da suke fama da yunwa a Amurka. Sai dai tsanantar yanayin bazuwar cutar COVID-19, ta sa Malama Haq da mijinta dukkansu suka rasa aikin yi, don haka yanzu ita ma ta shiga jerin mutanen da suke jiran samun kyautar abinci daga sassa dake raba irin wannan abinci.

Labarin Malama Haq ya nuna yadda marasa karfi a kasar Amurka ke fama da matsalar rayuwa. Alkaluman da hukumar kula da ma’aikata ta kasar Amurka ta gabatar, sun nuna cewa, yawan ‘yan kasar da suke neman dauki sakamakon rashin ayyukan yi, ya kai dubu 965 a ranar 9 ga watan Janairun bana, adadin da ya kai matsayin koli, tun daga watan Agustan bara. Hakika yawan mutanen da suke neman dauki sakamakon rashin aikin yi cikin makwannin da suka gabata a kasar Amurka, ya kan kai tsakanin dubu 700 zuwa dubu 900, wanda ya wuce jimillar dubu 200 da aka samu kafin barkewar annobar COVID-19.

Sai da a wani bangare na daban, ya zuwa tsakiyar watan Oktoban bara, kudin da attajiran kasar Amurka suka mallaka, ya kai dala triliyan 3.88, adadin da ya karu da dala biliyan 931, idan an kwatanta da jimillar da aka samu a watan Maris na bara.

Wadannan alkaluman sun nuna cewa, annobar COVID-19 ta kara haddasa gibi tsakanin al’ummar kasar Amurka, inda matakan farfado da tattalin arziki da gwamnatin kasar ta dauka suka sanya darajar kadarorin da wasu attajirai suka mallaka ta karu. Sa’an nan za su iya samun a yi musu gwajin cutar COVID-19, da allurar rigakafin cutar kafin ragowar ‘yan kasar. Yayin da a nasu bangare, karin marasa karfi a kasar ke fama da yunwa, da matsalar ganin likita a lokacin da suke da bukata.

Kafin haka, cibiyar nazarin harkokin al’umma mai zaman kanta ta Pew ta sanar a watan Yulin shekarar 2018 cewa, daga shekarun 1970, an fara samun yawaitar gibi a tsakanin masu kudi da marasa karfi na kasar Amurka. A shekarar 2020, mutane mafi samun kudi a kasar da yawansu ya kai kashi 1% na kasar sun mallaki kashi 30.5% na dukiyoyin dukkan magidantan kasar, yayin da attajiran da yawansu ya kai 10% na al’ummar kasar suka mallaki kashi 69% na kudin magidantan kasar. Amma a nasu bangare, marasa karfi a kasar, da yawansu ya kai kashi 50% na daukacin al’ummar kasar, sun mallaki kudin da ya kai kashi 1.9% na kudin magidantan kasar ne kawai.

Idan aka yi la’akari da yanayin da kasar Amurka ke ciki, inda take da marasa karfi kimanin miliyan 40, da mutanen da suka rasa matsugunansu dubu 500, da miliyoyin mutanen da suke fama da yunwa, za a fahimci cewa, tsarin siyasar kasar ba ya kula da marasa karfi da talakawa.

Ko da yake ‘yan siyasan kasar Amurka su kan yi ikirarin tabbatar da daidaito da adalci a kasar, amma yawaitar gibin da ake samu cikin al’ummar kasar na kara nuna musu cewa, akwai wasu matsaloli a cikin tsarin siyasar kasar na jari hujja.

Idan muka kalli tsarin siyasar kasar Amurka, za mu ga cewa, rukunai na attajirai da masu kudi suna tasiri matuka a harkokin siyasar kasar. Saboda haka, ba wani abun ban mamaki ba ne, yadda manufar farfado da tattalin arzikin kasar za ta fi fifita attajirai. Wani shehun malami a kasar Birtaniya ya taba bayyana cewa, dalilin da ya sa ake kara samun gibi cikin al’ummar kasar Amurka, shi ne wasu manyan manufofin da kasar take aiwatarwa, wadanda suka hada da mai da dukiyoyin al’umma karkashin mallakar daidaikon mutane, da raba dukiya bisa tsarin kasuwanci cikin ‘yanci, da kare moriyar masu abin hannunsu. Ta haka za mu iya ganin cewa, rashin daidaito cikin al’umma wata matsala ce da kasar Amurka ta kasa daidaita ta. (Bello Wang)

Bello