logo

HAUSA

Matsalar Wariyar Launin Fata Ta kara Raba Kan Al’ummar Kasar Amurka

2021-01-19 14:16:46 CRI

Matsalar Wariyar Launin Fata Ta kara Raba Kan Al’ummar Kasar Amurka_fororder_美国人权

Tsohon shahararren dan wasan kwallon kwando na kasar Amurka kuma dan asalin Afirka Kareem Abdul-Jabbar ya taba bayyana cewa, bakaken fata ba sa amfana da tsarin dimokuradiyya a kasar Amurka. Kalaman nasa ya bayyana yadda aka dauki shekaru dari 4 ana cin zalin al’ummu marasa rinjaye a Amurka, ya kuma nuna rashin sahihancin Amurka na shimfida tsarin dimokuradiyya, a kokarin nuna adalci ga kowa da kowa.

Yadda wasu masu bore suka kutse cikin ginin majalissar dokokin kasar Amurka ta “Capitol Hill” a kwanan baya, ya kara nuna ma’anar dimokuradiyya salon Amurka. Da farko wasu ‘yan sandan Amurka sun bar masu zanga-zanga sun shiga cikin Capitol Hill, daga baya sun dauki hoto da masu zanga-zangar, sa’an nan kashegari an yi zanga-zanga a wajen dakin tunawa da Abraham Lincoln, inda kusan babu ‘yan sanda ko masu tsaron al’ummar kasar. Matakan da 'yan sanda suka dauka kan masu zanga-zanga da suka mamaye ginin majalisar dokokin, wadanda galibinsu fararen fata ne, ya sha bamban sosai da yadda suka gallazawa masu zanga-zangar nuna adawa da yadda ake cin zarafin bakaken fata a watan Yunin bara.

Yadda 'yan sandan suke nuna bambancin launin fata, ya haifar da abubuwa da dama. Idan mun waiwayi tarihin Amurka, daga kashe ‘yan asalin kasar wato Red Indians zuwa fataucin ‘yan Afirka don su zama bayi, za mu gane cewa, lallai wariyar launin fata, wata muhimmiyar hanya ce da Amurka ta taba bi wajen raya kanta. Ya zuwa yanzu al’ummu marasa rinjaye ba su samu matsayinsu da kamata ya yi su samu a Amurka ba. Ana fama da wariyar launin fata ta hanyoyin aiwatar da doka ba bisa adalci ba, gibin da ke tsakanin masu kudi da matalauta, bambancin samun jinya da dai sauransu. Musamma ma yayin da ake fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19, a kasar Amurka, wadda ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya, alkalulman cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka masu yaduwa ta Amurka sun nuna cewa, yiwuwar mutuwa sakamakon annobar ta COVID-19 da Amurkawa ‘yan asalin Afirka suke fuskanta ta ninka sau 2.8 bisa na fararen fata.

Irin wannan bambancin na launin fata, ya shafi sassa daban daban na al’ummar kasar Amurka. George Floyd, wani Ba’amurke ne, dan asalin Afirka ya rasa ransa a hannun dan sanda farar fata a watan Yunin bara. Mutuwarsa tana daya daga cikin yawan munnan abubuwan da ‘yan sandan Amurka suka aikata kan al’ummu marasa rinjaye ba bisa adalci ba.

Har ila yau, ana ta kai wa al’ummu marasa rinjaye hari don nuna musu tsana a Amurka. Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2016, yawan mutanen da suka mutu sakamakon tsattsauran ra’ayi ya kai kashi 20 cikin dari na yawan mutanen da suka mutu sakamakon ta’addanci. Wannan adadi ya haura zuwa kashi 98 cikin dari a shekarar 2018.

Haka zalika, ana nuna wa marasa rinjaye bambanci a fannonin samun aikin yi, kudin albashi har ma da ba da rancen kudi. Alkaluman hukumar kididdiga ta ‘yan kwadagon Amurka sun nuna cewa, daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2018, matsakaicin albashin da Amurkawa bakaken fata suke karba a mako, kusan kasa da kaso 30 na fararen fata ne.

Hakika dai gwamnatin Amurka ta tsara manufofi masu yawa domin kiyaye hakkokin kabilu wadanda ba fararen fata ba. Ta kuma tsara dokar kiyaye hakkin al’umma, dokar harkokin zabe, dokar nuna adalci tsakanin al’umma da dai sauransu, amma wadannan manufofi sun bari wariyar launin fata ta kara haifar da rabuwar kai a tsakanin al’ummar kasar.

Dukkan jam’iyyun siyasa 2 na Amurka, wadda ta lashe mulkin kasar, ba ta so ta warware matsalar wariyar launin fata. Duk lokacin da aka samu rikicin al’umma, to, jam’iyyun 2 su kan kwantar da hankulan jama’a bisa hujjar siyasa maras amfani, a yunkurin boye dukkan matsalolin da ake fama da su karkashin tsarin dimokuradiyya mai salon Amurka. Don haka wariyar launin fata ta zama ruwan dare a Amurka. Ta kan fusata al’umma a ko da yaushe tare kuma da kara raba kan al’ummar kasar ta Amurka. Tuni kasashen duniya suka kara fahimtar cewa, tsarin dimokuradiyya salon Amurka, wani nau’in wasan siyasa ne da wasu mutane suke yi. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan