logo

HAUSA

Matakin GDPn kasar Sin ya yi matukar bunkasa a shekarar bara

2021-01-18 19:46:54 CRI

Matakin GDPn kasar Sin ya yi matukar bunkasa a shekarar bara_fororder_微信图片_20210118164908

Tun daga farkon shekarar 2020 da ta shude, tattalin arzikin duniya ya shiga wani mawuyacin hali da rashin tabbas sakamakon barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19. Sai dai kamar yadda masu hikimar magana ke cewa, “mai rabon ganin badi ko ana muzuru ana shaho sai ya gani.” Duk da irin matsanancin halin da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, hukumomin kasar Sin sun dauki jerin matakai iri daban daban domin yin kandagarkin karayar tattalin arzikin kasar. Ko shakka babu, matakan da kasar ta dauka sun taka muhimmiyar rawa wajen kyautata makomar tattalin arzikin kasar.

Kamar yadda wasu alkaluma da hukumar kididdigar kasar Sin (NBS) ta fitar a Litinin din nan sun nuna cewa, GDPn kasar ya karu da kaso 2.3 a shekarar 2020, bisa makamancin lokaci na bara, inda ya haura kudin kasar Yuan Triliyan 101.5986, kwatankwacin dala triliyan 15.42. Alkaluman hukumar sun nuna cewa, saurin ya zarce karuwar kaso 0.7 da aka samu a watanni tara na farkon shekarar. A rubu’i na hudu na shekarar 2020 kuwa, GDPn kasar ya karu da kaso 6.5 cikin 100, idan an kwatanta da makamancin lokaci na bara, saurin karuwar ya zarce kaso 4.9 na bunkasar da aka samu a rubu’i na uku na shekara. Hukumar ta kara da cewa, harkokin tattalin arzikin kasar ya farfado yadda ya kamata, inda ayyukan yi da hada hadar yau da kullum, da zamantakewar jama’a duk sun inganta. Haka kuma, an yi nasarar kammala manyan ayyukan dake shafar tattalin arziki, da jin dadin jama’a fiye da yadda aka yi hasashe.

Dama dai, batun kyautata rayuwar jama’a shi ne wani muhimmin batu da mahukuntan Sin suka sha nanatawa. Alkaluman hukumar sun kara nuna cewa, kasuwar aikin yi ta kasar Sin ta daidaita a shekarar ta 2020, inda bincike da aka gudanar game da rashin aikin yi a yankunan biranen kasar, ya tsaya kan kaso 5.6, kasa da abin da gwamnati ta yi fatan cimmawa a shekara na kimanin kaso 6 cikin 100. Koda a makon da ya gabata ma, bayanai sun nuna cewa matsayin cinikayyar kayayyakin Sin a ketare ya kai matsayin koli a shekarar 2020 duk da kalubalolin da aka fuskanta. Kididdiga ta nuna cewa, jimillar kayayyakin shigi da ficin na kasar Sin a shekarar 2020, ya karu da kaso 1.9 zuwa yuan triliyan 32.16, kwatankwacin dala triliyan 5, adadin da ya kai matsayin koli duk da matsalar jigilar kayayyaki da aka samu a duniya. A cewar kakakin hukumar kwastan ta kasar Sin, Li Kuiwen, duk da kalubalen tattalin arziki da cinikayya da aka fuskanta a shekarar 2020, kasar Sin ta zama kasa daya tak a duniya da ta samu ci gaba ta fuskar cinikayyar kayayyaki a ketare. (Ahmad Fagam)