logo

HAUSA

Babban Sabani A Tsakanin Jam’iyyun Amurka Zai Lalata Harkokin Kasa

2021-01-15 21:03:49 CRI

Babban Sabani A Tsakanin Jam’iyyun Amurka Zai Lalata Harkokin Kasa_fororder_210115-sharhi-maryam-hoto

A ranar Laraba majalisar wakilan Amurka ta jefa kuri’ar tsige shugaban kasar Donald Trump, bisa tuhumarsa da laifin tunzura mabiyansa wajen tada bore a zauren majalisar a makon jiya, shugaba Trump ya shiga cikin tarihin zama shugaban Amurka na farko, da aka tsige har sau biyu daga mukamin shugabancin kasar. Masu nazarin na ganin cewa, an dauki wannan mataki ne domin toshe duk wasu hanyoyin da mai yiyuwa Trump zai yi amfani da su wajen dawo wa shugabancin kasar.

Tashe-tashen hankulan da suka faru a kasar Amurka, sun nuna babbar matsalar tsarin zaman takewar al’ummar kasar, da sabanin dake tsakanin wasu manyan mutane da ma jam’iyyun kasar. Rahotanni na cewa, a halin yanzu, ana fuskantar babban sabanin siyasa a wannan kasa. Kamar yadda masani a jami’ar Cambridge Martin Jacques ya ce, yanzu, kasar Amurka tana fama da mummunan sabani a tsakanin jam’iyyar Republic da jam’iyyar dimocrate, har ba su iya magana yadda ya kamata, lamarin da zai haddasa rugujewar gwamnatin kasar baki daya a nan gaba.

Jami’yyun kasar biyu na kare muradunsu fiye da muradun kasa da na al’ummar kasar, har sabanin dake tsakaninsu ke ci gaba da karuwa. Duk da babbar matsalar yaduwar annobar cutar COVID-19 dake addabar kasar, jam’iyyun biyu ba su daina fadace-fadace a tsakaninsu ba. Lamarin da ya hana aikin samar da kayayyakin yaki da annoba bisa ka’ida, da adalci, hakan ya sa, ya zuwa yanzu, Amurkawa sama da miliyan 23 sun kamu da cutar, yayin da mutane dubu 380 suka rasa rayukansu.

Idan kasar Amurka ba ta warware wannan matsala yadda ya kamata ba, duk wata maganar game da hada kan al’ummar kasar, maganar ce maras ma’ana. Tabbas, karuwar sabanin dake tsakanin jami’yyun biyu za ta gurgunta harkokin kasar ta Amurka bi da bi. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)