logo

HAUSA

Cinikayyar Kayayyakin Sin A Ketare Ya Taimaka Ga Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya

2021-01-14 22:07:16 CRI

Cinikayyar Kayayyakin Sin A Ketare Ya Taimaka Ga Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya_fororder_210114-sharhi-maryam-hoto

Hukumar kwastam ta kasar Sin ta gabatar da takaitaccen bayani kan cinikayyar kayayyakin Sin a ketare ta shekarar 2020, wadda ta sami sakamako masu gamsarwa matuka. Gabanin kalubalen yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 da raguwar cinikin dake tsakanin kasa da kasa, ci gaban cinikayyar Sin a ketare ya kara farfado da tsarin samar da kayayyakin na duniya.

Cikin farkon watanni uku na shekarar 2020, jimilar kayayyakin shige da fice na kasar Sin ta ragu sakamakon barkewar cutar COVID-19, sa’an nan, ta fara kankama, sakamakon managartan matakai da kasar Sin ta dauka wajen dakile yaduwar annobar cutar.

Alkaluman kiddidiga na nuna cewa, jimilar kayayyakin shige da fice na kasar Sin a shekarar 2020, ya karu da kaso 1.9 zuwa yuan triliyan 32.16. lamarin da ya sa, kasar Sin ta kasance kasa daya tilo cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, wadda ta samu karuwar cinikayyar kayayyakin shige da fice.

Bisa bayanin gwamnatin Sin, adadin kayayyakin tufafi da na’urorin jinya da magunguna da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen ketare, ya karu da 31%, yayin da adadin kwamfuta da na’urorin laturoni da ta fitar ya karu da 22.1%. Wadannan kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen ketare sun biya bukatun kasa da kasa wajen yaki da cutar COVID-19, da kuma biyan bukatun al’ummomin kasa da kasa yayin da suke zaman gida. Wannan wata babbar gudummawa ce da kasar Sin ta bayar wajen yaki da annoba a kasashen duniya.

A fannin shigar da kayayyaki kuma, a cikin shekarar 2020, adadin man fetur da kasar Sin ta shigo da shi ya karu da 7.3%, kana, adadin wasu sinadarai da Sin ta shigo da shi ya karu da 7%, kuma adadin hatsin da ta shigar cikin kasar, ya karu da 28%, yayin da adadin naman da ta shigo da shi cikin kasar ya karu da 60.4%。

Cikin wannan shekara ta musamman, jimillar kayayyakin shige da fice ta karu cikin yanayin zaman karko, sabo da karfin tattalin arzikin kasar, da kokarin dukkanin al’ummomin Sin. Wannan ba kawai ya nuna karfin kasar Sin wajen fuskantar kalubaloli iri-iri ba, har ma ya daga matsayin kasar Sin a fannin tsarin samar da kayayyaki a kasashen duniya.

Lamarin da ya nuna mana cewa, za a gaggauta farfadowar tsarin samar da kayayyaki a duniya ta hanyar yaki da annoba cikin hadin gwiwa da bude kofa ga waje, cikin wannan sabon zamani da kasashen duniya ke kara dunkulewa wajen guda. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)