An kaura zuwa sabon kauye
2021-01-14 15:22:20 CRI
Kauyen Longya da ke yankin Guoluo mai zaman kansa na kabilar Zang da ke lardin Qinghai na kasar Sin yana da magidanta makiyaya 67 wadanda a baya aka yi rajistarsu a matsayin masu fama da talauci, wadanda suke zaune a cikin tsaunukan da ke fuskantar wahalar zirga-zirga da kuma yanayin rayuwa mai tsanani. Ya zuwa shekarar 2016, an kaurar da magidantan zuwa sabon kauyen da aka gina musu, inda aka samu saukin zirga-zirga, baya ga ruwa da wuta da aka samar musu.(Lubabatu)