An gano wasu goggon birai da suka kamu da cutar COVID-19 a Amurka
2021-01-14 10:53:03 CRI
An gano wasu goggon birai da suka kamu da cutar COVID-19 a wani gidan dabbobi na birnin San Diego da ke Amurka. Ana ganin cewa, wannan ne karo na farko da aka gano dabbobi dake shayar da nono da suka harbu daga cutar.