logo

HAUSA

Kakar kasashe masu tasowa ta kusa yanke Saka

2021-01-13 19:25:15 CRI

Kakar kasashe masu tasowa ta kusa yanke Saka_fororder_微信图片_20210113192145

Yanzu haka dai, wasu kasashe sun fara cin gajiyar alluran riga kafin COVID-19 da wasu kamfanonin harhada magunguna suka samar, matakin da ake fatan zai kai ga rage tasirin irin illar da wannan annoba ta haifarwa duniya.

Sai dai wani abin takaici shi ne, wasu kasashen yamma na kokarin saye baki dayan alluran rigakafi, don amfanin jama’arsu ba tare da yin la’akari da kasashe masu tasowa da marasa karfi da ba za su iya sayen riga kafin ba, da ma siyasantar da batun.

Wannan ne ma ya sa, tun farko kasar Sin ta yi alkawarin cewa, da zarar an kammala gwaji, da sanarwa har ma aka fara amfani da riga kafin da ta samar, to, za ta fara samarwa kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka. Sannan dukkan al’ummomin duniya za su amfani da shi ba tare da gindaya wani sharadi na siyasa ba.

Abin farin ciki shi ne, a kwanakin baya mahukuntan kasar Sin, sun sanar da ba da umarnin cinikayyar nau’in farko na alluran rigakafin cutar numfashi ta COVID-19, wanda aka samar a cikin kasar bisa sharadi.

Rigakafin wanda hukumar lura da magunguna ta kasar Sin NMPA ta ba da umarnin cinikayyarsa, kamfanin Beijing Biological Products Institute ne ya samar da shi, wanda ke karkashin gungun kamfanonin “China National Biotec Group” ko CNBG, mai alaka da kamfanin Sinopharm.

Rahotanni na tabbatar da cewa, sakamakon wucin gadi na gwaji a zagaye na 3 na rigakafin da aka yiwa mutane, ya shaida amfanin rigakafin ya kai kaso 79.34 bisa dari, wanda ya kai mizanin da WHO, da NMPA suka gindaya kafin fara amfani da ko wane nau’i na rigakafi.

A yayin rangadin baya-bayan da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya kai kasashen Afirka biyar, an yiwa shugaban kasar Botswana allurar riga kafin COVID-19 da kasar Sin ta samar, abin da ke kara nuna ingancin riga kafin. A halin da ake ciki kuma, kasar Masar ta sanar da cewa, ta bayar da lasisin amfani da allurar riga-kafin annobar COVID-19 wadda kamfanin hada magunguna na kasar Sin Sinopharm ya samar a hukumance domin amfanin gaggawa a kasar, bayan kasar ta karbi kason farko na riga kafin SinoPharm.

Ana sa ran ita ma gwamnatin Najeriya da wasu kasashen Afirka har ma da Thailand, sun bayyana shirinsu na sayen alluran riga-kafin COVID-19 miliyan biyu wanda kamfanin hada magunguna na kasar Sinovac Biotech ya samar.

Abin dake kara nuna cewa, kasashe masu tasowa, ba za su samu wata matsalar samun rigakafin COVID-19 ba, ko da manyan kasashe irinsu Amurka, ba su samar musu alluran da aka samar ba. Mai Uwa a gindin Murhu, ba zai ci Gaya ba. (Ibrahim Yaya)