Kauyen kabilar Jino da ke yayata fasahar dinkin hannu
2021-01-13 13:46:58 CRI
Nan wani kauye ne na ‘yan kabilar Jino da ke lardin Yunnan na kasar Sin, inda mazauna kauyen suka hada kai suka kafa wani kamfani na samar da kayayyakin dinkin hannu, kamfanin da a hannu daya ya yayata fasahar dinki ta gargajiya ta ‘yan kabilar, tare da kara kudin shigar mazauna kauyen.