logo

HAUSA

Kasar Sin, Aminiyar Afirka, Ta Dauki Ingantatun Matakan Ci Gaban Afirka

2021-01-12 19:30:13 CRI

Kasar Sin, Aminiyar Afirka, Ta Dauki Ingantatun Matakan Ci Gaban Afirka_fororder_sin01

Yayin ziyararsa a nahiyar Afrika a makon da ya gabata, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya sanar a kasar Tanzania cewa, yayin taron FOCAC da za a yi bana, za a daukaka dangantakar Sin da Afrika bisa wasu fannoni 7. Lallai kasar Sin, wato aminiyar kasashen Afirka, ta mayar da hankali wajen zabo ingantattun bangarorin da za su shafi dukkan harkokin rayuwa tare da samar da ci gaba ga nahaiyar da al’ummarta maimakon maganganun banza kamar “kare ’yancin ’yan Afirka ko shimfida dimokuradiyya a Afirka” ko “kada ku yi hadin gwiwa da wata kasa daban” kamar yadda wasu ’yan siyasar yammacin kasashen duniya su kan yi.

A lokacin da Mr. Wang Yi yake ganawa da manema labaru na Afirka, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwa a bangaren kiwon lafiya da nahiyar Afrika, da nufin ganin bayan annobar COVID-19 baki daya. Kasashen Afrika da Sin na da kamaceceniya ta fannoni da dama, kuma daga cikinsu akwai na yawan jama'a. Ganin irin yadda wannan annoba take kisa tare da yaduwa kamar wutar daji, da kuma irin nasarorin da Sin ta samu wajen dakile yaduwarta, hadin gwiwar bangarorin biyu zai bada ma'ana sosai. Idan kasashen suka samu dabaru da ilimin yaki da cutar, za su dakile yaduwarta a tsakanin al'ummominsu da ma na wasu yankunan. Ban da haka, zai sa su zama cikin shiri da samun ilimi kan irin wannan annoba idan an sake samun makamanciyarta. Yadda Sin ke taimakawa wajen gina hedkwatar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka, ba aiki ne da zai tsaya ga tinkarar COVID-19 ba kadai, abu ne da zai haifar da alfanu mai dogon zango. Har ila yau, hadin gwiwar su a wannan fanni, zai sa kowannensu ya fahimtar yanayin cutar a yankuna daban daban, lamarin da zai bayar da dama wajen kare lafiya da rayukan Jama'ar bangarorin biyu. Ma'ana, hadin gwiwar za ta sa kwararru a nahiyar Afrika su fahimci yanayin cutar a kasar Sin, ta yadda idan Sinawa na Afrika, za su samu tabbacin kiwon lafiya, haka ma idan ’yan Afrika suna kasar Sin.

Na biyu, Sin za ta bunkasa karfin samar da kayayyaki. Wato za ta taimakawa nahiyar kara karfinta, domin dogaro da kanta wajen samar da kayayyaki kirar Afrika. Hakika Sin ta yi hangen nesa kamar yadda ta saba. Idan har aka cimma wannan buri, to kasahen nahiyar za su iya dogaro da kansu maimakon yadda suke dogaro da kayayyakin da ake shigar musu daga ketare. Lamarin da zai bunkasa tattalin arzikinsu da samar da kayyayaki cikin farashi mai rahusa. Wannan zai kara inganta rayuwa jama'a dake fuskantar matsin rayuwa saboda tsadar kayayyaki. Ban da haka, zai ba kasashen nahiyar damar lalubo damarmakin da suke da su da amfani da albarkatun da suke da arzikinsu. Har ila yau, wannan mataki zai samar da dimbin ayyukan yi ga mutane musammam matasa. Kuma idan matasa suka samu aikin yi, to za a samu gagarumar raguwar aikata laifuffuka.

Na uku, kasar Sin za ta karfafa hade kasashen nahiyar ta fuskar ababen more rayuwa, da hada gwiwar ciniki cikin ’yanci a tsakaninsu. Ababen more rayuwa na da muhimmanci ga kowacce kasa dake neman ci gaba. Wannan batu ya zo a kan gaba, wato daidai lokacin da aka fara aiki da yarjejeniyar cinikayya cikin ’yanci ta nahiyar. Ginin ababen more rayuwa a nahiyar zai saukaka jigilar kayayyaki da mutane tsakanin kasa da kasa a nahiyar. Sannan, zai kara jan hankalin masu zuba jari tare da kara musu kwarin gwiwa kan nahiyar.

Na hudu, Sin za ta inganta hadin gwiwarsu a bangaren aikin gona, ta yadda nahiyar Afrika za ta zama mai wadatar amfanin gona. Kasar Sin ta yi fice a fannin fasahohin zamani. Kasashen Afrika na da burin ciyar da kansu, sai dai akwai karancin fasahohin saukaka aikin. Hadin gwiwa a wannan bangare zai ba manoma da karin mutanen dake sha'awar harkar, kwarin gwiwar bada tasu gudunmawa. Bisa hadin gwiwar, manoma za su kara rungumar noma domin zama cikakkiyar sana'a. Sannan nahiyar za ta yi adabo da yunwa da samun wadatuwar abincin da za ta ciyar da al'ummarta.

Na biyar, Sin za ta karfafa hadin gwiwarsu a bangaren fasahohin zamani, domin samar da nahiyar Afrika mai tafiya da zamani. A wannan lokaci na wayewar kan bil adama, dole ne kasa ta rungumi fasahohin zamani idan har ta na son samun ci gaba, sannan a rika jin amonta a duniya. Ci gaban kasar Sin ba sabon abu ba ne a wajen al'umma duniya. Sin ta zama abar koyi ta kowacce fuska, don haka, hadin gwiwa da Sin a fannin fasaha, abu ne da ya dace da kasa da kasa, domin samun gagoewarta da dabarun da suka kai ta ga taka matsayin da ta kai a yanzu

Na shida, za su hada gwiwa a bangare kare muhalli, domin gina nahiya mai rayawa da kiyaye muhalli. Kare muhalli abu ne da ko da yaushe ake magana akai. Duk ci gaban da kasa za ta samu, muddun bata kare muhallinta ba, to kamar an yi ba a yi bane. Kasar Sin na da tarin dabarun kare muhalli, kuma kasashen Afrika, za su iya koyi daga fasahohinta kamar na bola jari da rage sinadarai masu gurbata muhalli domin kyautata zaman rayuwa tsakanin bil adama da muhalli da sauran halittu.

Na karshe shi ne, kara karfafa hadin gwiwa wajen tsaron aikin soja, domin tabbatar da tsaro a nahiyar Afirka. Kowa ya san yadda ake fama da rashin tsaro a duniya, kuma idan ana kirga kasashen da suka samu ci gaba a fannin tsaro, to Sin tana gaba-gaba. Don haka, wannan mataki zai yi gagarumin tasiri a kokarin da kasashen nahiyar ke yi na tabbatar da tsaro. Hakika kasar Sin tana da dabaru da matakai daban daban da suka kai ta ga inda take a yanzu, don haka, koyi da ita ko hadin gwiwa, za ta saita kasashen nahiyar Afrika kan tafarkin da ya dace. (Fa’iza Muhammad Mustapha)

Fa’iza Muhammad Mustapha