logo

HAUSA

Allah daya gari bamban: Abin da na tuna bayan da na kalli wasu hotuna 2

2021-01-08 19:29:49 CRI

Allah daya gari bamban: Abin da na tuna bayan da na kalli wasu hotuna 2_fororder_微信图片_20210108192855

Wadannan hotuna 2 sun nuna abubuwan da suka faru a Laraba 6 ga wata, a kasashen 2, wato Sin da Amurka. Wadanda suka shaida mabambantan yanayin da ake ciki a kasashen 2.

A bangaren hagu, muna iya ganin yadda wasu malamai da dalibai na jami’ar nazarin ilimin teku ta birnin Dalian na kasar Sin suna kokarin jigilar kayayyaki yayin da ake samun dusar kankara da take saukowa daga sama. Tun daga watan Disambar bara, an sake gano masu kamuwa da cutar COVID-19 a birnin Dalian, daga bisani an dauki matakan hana yaduwar cutar cikin gaggawa a birnin, inda zuwa ranar Larabar da ta gabata, yawan mutanen da suka harbu da cutar a birnin ya kai 82, sa’an nan adadin ya daina karuwa. Duk da haka, mutanen birnin ba su yi kasala ba. Misali a jami’ar nazarin ilimin teku ta Dalian, malamai da daliban jami’ar fiye da mutane 13,000 har yanzu suna kokarin zaman gida. Yayin da wasu daga cikinsu ke daukar nauyin jigilar abinci da sauran kayayyakin da ake bukata, gami da raba su ga kowa. An dauki hoton ne a lokacin da wadannnan masu aikin sa kai suke kokarin gudanar da aikinsu, ba tare da tsoron yanayi mai matukar sanyi da yawan dusar kankara ba.

Sa’an nan hoton dake bangaren dama ya nuna yadda masu bore suke kokarin neman kutsa kai cikin zauren majalisar dokokin kasar Amurka, yayin da ’yan majalisar ke kidaya kuri’un wakilan masu zabe na zaben shugabancin kasar da ya gudana a shekarar da ta gabata, a birnin Washington, duk a ranar Laraba. Bayan da shugaba Donald Trump ya fadi a babban zaben kasar, ya fara zargin an tabka magudi a zaben, koda yake, tuni kotunan Amurka a matakai daban-daban suka yi watsi da zargin. Sa’an nan a ranar Laraba, ya bukaci magoya bayansa su yi zanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar. Daga bisani, dimbin jama’a magoya bayansa sun mamaye ginin majalisar dokokin da ake kira Capitol, inda suka yi fito-na-fito da ’yan sanda, tare da haddasa rasa rayukan fararen hula 4. 

A cikin rana daya ne mabambantan abubuwan suke abkuwa a kasashen Sin da Amurka, inda suka nuna abin da aka fi maida hankali a kai a kasashen 2. A kasar Sin batun shi ne kula da rayuka, da lafiyar jikin jama’a. Yayin da a kasar Amurka, wannan abu shi ne moriya a fannin siyasa.

Bayan da aka gano barkewar cutar COVID-19 a kasar Sin a farkon shekarar 2020, hukumomin kasar sun dauki kwararan matakai wajen dakile yaduwar cutar, da ceton rayukan jama’a. Tun daga lokacin har zuwa yanzu, sannu a hankali an samu shawo kan yanayin yaduwar cutar sosai a kasar, tare da farfado da tattalin arziki, ta yadda mutanen kasar suke iya zama cikin kwanciyar hankali, da ci gaba da jin dadin zaman rayuwarsu. Idan an samu sake bullar cutar a wani wurin kasar, sai a dauki matakai na kandagarkin cutar cikin gaggawa, don tabbatar da cewar za a ba da kulawa ga masu harbuwa da cutar nan take, kana cutar ba za ta bazu a cikin kasar ba.

A nata bangare, kasar Amurka ta fada cikin rudani sosai a fannin tinkarar annobar COVID-19. Ko da yake, kasar ta fi karfin tattalin arziki a duniya, da samun fasahohin aikin jinya mafi inganci. Amma wadannan abubuwa ba su hana ta tsunduma cikin mawuyacin hali ba. Zuwa yanzu mutane fiye da miliyan 22 daga cikin al’ummar kasar ne suka harbu da cutar COVID-19, kana wasu fiye da dubu 370 suka rasa rayukansu.

Ganin haka zai sa mutum mamaki, gami da sha’awar sanin dalilin da ya sa haka. To, dubi abubuwan da wasu ’yan siyasan kasar Amurka suka aikata, za a samu karin haske dangane da batun. Ga alamar wadannan ‘yan siyasa sun fi dora muhimmanci kan moriyar kansu, maimakon rayukan jama’arsu. Inda a maimakon daukar kwararan matakai masu dacewa, su kan watsa wasu bayanai na jabu don yaudarar jama’a. Maimakon su umarci jama’ar su zama a gida don magance harbuwa da cutar, suna watsa wasu kalamai na ruruta wuta, don neman jama’a su shiga tituna, har ma su tada bore a kasar, tare haddasa rasa rayukan mutane.

Abin ban mamaki shi ne, har yanzu wasu ’yan siyasan kasar Amurka suna zargin kasar Sin da keta hakkin dan Adam. Amma mene ne hakkin dan Adam na tushe? Ba shi ne hakkinsu na rayuka ba? Idan an kalli hotunan 2 dake sama, za a san a ina aka fi girmama hakkin mutane na rayuka, Amurka, ko kuma kasar Sin. (Bello Wang)

Bello