logo

HAUSA

Sharhi: Rikicin da ya faru a Amurka ya shaida aibin kasar ta fannin dimokuradiyya

2021-01-08 14:17:42 CRI

Tsarin dimokuraddiya abu ne da kullum ‘yan siyasar Amurka suke alfahari da shi, wadanda kuma suke kokarin yayata tsarinsu a sassan duniya daban daban, tare da hura wutar rikici. Amma idan an dubi irin rudanin da kasar ta Amurka ita kanta ta shiga a halin yanzu, lallai za a gano aibin kasar ta fannin dimokuradiyya.

A ranar 6 ga wata, agogon wurin, majalisun dokoki na kasar Amurka sun gudanar da taro na kidayar kuri’un wakilan masu zabe mai alaka da zaben shugaban kasar da aka kada a jihohi daban daban na kasar, lamarin da ya haifar da zanga-zanga, inda kuma mutane hudu suka halaka a sanadin rikicin. A sakamakon rikicin kuma, an kafa dokar hana fitar dare a birnin Washington, matakin da ba safai a kan dauke shi ba.

Bana ya cika shekaru 10 da aukuwar tashe-tashen hankali a wasu kasashen Larabawa, tashe-tashen hankali da suka kifar da gwamnatocin kasashen yammacin Asiya, da arewacin Afirka da dama, bisa ga yadda wasu kasashen yamma suka sa hannunsu a ciki.

Duk da haka, bayan tashe-tashen hankalin, akasarin al’ummar kasashen sun gano cewa, wahalar da ba ta karewa ce kawai suka samu, daga abin da ake kira wai “tsarin dimokuradiyya” na Amurka, a maimakon alheri.

A hakika, a yayin da Amurka din ke zargin sauran kasashen da “rashin samun dimokuradiyya”, tare da kakaba musu takunkumi, da kifar da gwamnatocinsu, ya kamata ta dubi halin da ta samu kanta a ciki, kuma ta daina haifar da matsaloli ga sauran kasashen duniya.(Lubabatu)