logo

HAUSA

Ziyarar Wang Yi a Afirka na kunshe da babban Albishir

2021-01-07 16:34:05 CRI

Ziyarar Wang Yi a Afirka na kunshe da babban Albishir_fororder_0107-1

Ga duk mai bibbiyar yanayin da ake ciki a fannin hadin gwiwar Sin da kasashen nahiyar Afirka, ya kwana da sanin dankon zumunta, da goyon baya da sassan biyu suka jima suna yiwa juna.

A bana, cikin muhimman abubuwan tarihi da aka bude wannan shekara ta 2021 da su, game da alakar Sin da Afirka, shi ne ziyarar da dan majalissar gudanarwa, kuma ministan wajen kasar Wang Yi ke yi yanzu haka a kasashen Najeriya, da JD/Congo, da Botswana, da Tanzania, da Seychelles.

Najeriya ce dai zangon farko da Wang Yi ya fara isa a ranar Litinin, karkashin wannan ziyara aka kwashe shekaru 31 ana gudanar da ita, kuma babban jami’in ya sauka birnin Abuja fadar mulkin kasar da wani muhimmin albishir, inda yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ya halarta tare da takwaransa na Najeriya Geoffery Onyeama, Mr. Wang ya bayyana aniyar Sin ta ci gaba da goyon bayan kasashen Afirka, a yakin da suke yi da cutar COVID-19, ciki har da batun samarwa nahiyar isassun alluran rigakafin cutar cikin sauki kuma a kan lokaci.

A lokaci guda kuma, Sin ta sha alwashin goyon bayan kasashen Afirka, ciki har da Najeriya, wajen aiwatar da matakan gaggauta farfado da tattalin arzikinsu, karkashin shawarar nan ta "Ziri daya da hanya daya", ta yadda kasashen nahiyar za su kai ga samun daidaiton tattalin arziki, da tabbacin guraben ayyukan yi, da kyautata yanayin rayuwar jama’ar su.

Har ila yau, ya ce Sin za ta ci gaba da bunkasuwa, da daga matsayin hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka. Karkashin hakan, sassan biyu za su kira sabon taron dandalin hadin gwiwarsu a wannan shekara ta 2021. Bugu da kari, Sin za ta tabbatar da goyon bayanta ga kasashen Afirka, a fannin samun karin ikon fada a ji a harkokin kasa da kasa, kana ta shirya karfafa tattaunawa da nahiyar, game da batutuwan da suka shafi kasa da kasa da kuma shiyya shiyya a kan lokaci.

Ko shakka babu, wadannan matakai da Sin ta alkawarta aiwatarwa ga kasashen Afirka babban Albishir ne, musamman a gabar da kasashen nahiyar ke shan fama da radadin cutar COVID-19, da koma baya da annobar ta haifar. Tuni kuma masharhanta suka fara jinjinawa wannan ziyara, wadda a karshenta, ake fatan tattara sakamako mai gamsarwa, na kara ingancin alakar Sin da kawayen ta dake nahiyar Afirka. (Saminu Hassan)