logo

HAUSA

Kalaman Da ’Yan Siyasan Amurka Ke Yi Kan Jihar Tibet Ta Sin, Maganar Banza Ce

2021-01-05 13:38:36 CRI

Kalaman Da ’Yan Siyasan Amurka Ke Yi Kan Jihar Tibet Ta Sin, Maganar Banza Ce_fororder_210105-sharhi-maryam-hoto

Kwanan baya, shugaban kasar Amurka ya sa hannu kan “dokar nuna goyon baya da manufofin dake shafar jihar Tibet na shekarar 2020”, kuma, wasu ‘yan siyasan kasar Amurka sun yi zargin kasar Sin game da manufofin kabilu da addinai na kasar, da tsoma baki cikin harkokin zaben magajin shugaban addinin Buddha na kabilar Tibet, burinsu shi ne, bata yanayin tsaro da hana ci gaban jihar Tibet ta kasar Sin, da kuma dana wani tarko ga gwamnatin kasar Amurka dake tafe.

Batun jihar Tibet batu ne dake shafar ‘yanci da cikakken zaman kasar Sin, tsokacin da ‘yan siyasan kasar Amurka suka yi kan batun jihar, ya keta dokar kasa da kasa da ka’idar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, dukkanin maganganun da suka fada kan jihar Tibet ta kasar Sin, maganar banza ce.

Dokar wanda zai gaji shugaban addinin Buddha cikkakiyar doka ce, wadda ta dace da ka’idojin addinin Buddha da tarihin kasar Sin, kuma harkokin dake shafar magajin shugaban addinin Buddha, harkokin cikin gidan kasar Sin ne, wadanda suka shafi ‘yancin kasa, da ikon gwamnati, da ka’idojin addinai da ma mabiyansu, ba kamar yadda ‘yan siyasan kasar Amurka suke fada ba, wai magajin shi kadai yana da ikon aiwatar da ayyukan da abin ya shafa bisa doka. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)