Wani dan kasar Thailand na kokarin maida gashin kaza a matsayin naman shanu
2021-01-01 11:00:42 CRI
Duniya ba ta karewa da abin mamaki. Ga yadda wani dan kasar Thailand ke maida gashin kaza a matsayin naman shanu. Wannan bawan Allah ya gano cewa, ana zubar da gashin kaza kimanin ton miliyan 2.3 a ko wace shekara, amma ana iya sake amfani da su wajen hada abinci. Ya ce, akwai sinadari mai gina jiki a cikin gashin kaza, idan ana iya tace sinadarin, to za a taimaka wajen rage barnar da ake yi. Naman da ake yi da gashin kaza ba shi da dandano ko kadan, sai dai a yi amfani da magi.(Kande Gao)