logo

HAUSA

Sin Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Duk Da Ta Fuskanci Kalubale

2020-12-31 15:50:15 CRI

Sin Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Duk Da Ta Fuskanci Kalubale_fororder_微信图片_20201231154651

A Shekarar 2020 an fuskanci barkewar cutar COVID-19 da ta addabi duniya baki daya, ana kuma kokarin farfado da tattalin arzikin duniya, to yaya za a magance wadannan wahalhalu? Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana amsa iri ta kasar Sin.

Matsayin da Sin ta dauka wajen dakile cutar shi ne “Hadin kai”, matakin da ya tara karfin duk fadin duniya. A sa’i daya kuma, Sin ta sauke nauyin dake wuyanta ta hanyar baiwa sauran kasashe tallafin jin kai. Ya zuwa karshen watan nan da muke ciki, Sin ta baiwa kasashe fiye da 150 da kungiyoyin kasa da kasa 9 tallafi, tare kuma da tura tawagogin jiyya 36 zuwa kasashe 34.

Ban da wannan kuma, a matsayin kasar dake sahun gaba wajen nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19, Sin ta shiga shirin samar da allurar a duniya, don kokarin rarraba allurar bisa adalci da daidaito a duniya. Kasashe masu tasowa ciki hadda Brazil da Masar da sauransu sun riga sun samu allurar da Sin ta samar.

A cikin wannan shekara da aka shiga mawuyacin hali, Sin ta bayyanawa duk duniya cewa, ta zama zarafi da aboki ga kasashen duniya a maimakon barazana da abokiyar takara, duba da matakan da take dauka. (Amina Xu)