logo

HAUSA

Darashin COVID-19 ga bil Adama

2020-12-31 19:10:09 CRI

Darashin COVID-19 ga bil Adama_fororder_微信图片_20201231153236

A halin da ake ciki yanzu haka, annobar cutar COVID-19 na ci gaba da haifar da mummunan illa ga rayuwar bil Adama, inda karin mutane masu yawan gaske ke ci gaba da harbuwa da cutar.

Baya ga asarar rayuka da ake fuskanta, cutar ta kuma gurgunta yanayin rayuwa da aka saba da shi, ta dakile kyakkyawar zamantakewa, da tafiye tafiya, ta kuma takawa wasu manyan sassan cinikayya da harkokin raya tattalin arziki birki. Hakan ya jefa ayar tambaya a zukatan masharhanta da dama, game da ko yaya duniya za ta kasance bayan wannan annoba?

Daya daga sabbin kalubale da ake fuskanta a yanzu haka, shi ne gano sabbin nau’oin cutar da aka yi a wasu kasashen duniya, wanda hakan ya haifar da halin rashin tabbas, don gane da tasirin da ake hasashen alluran rigakafin cutar da ake samarwa yanzu haka ka iya yi.

A hannu guda kuma, akwai masu tunanin cewa, mai yiwuwa manyan kasashe mafiya karfi, za su mallake alluran da ake samarwa domin kan su, ta yadda za a bar kasashe marasa wadata ba tare da samun alluran a kan lokaci ba.

Wannan kalubale ne da ya kamata a dauki matakan shawo kan sa. Domin kuwa, a kasashe da dama da suka samu shawo kan cutar ta hanyar daukar matakan kandagarki, shigar baki da ‘yan kasa masu komawa gida dauke da cutar na mayar da hannun agogo baya. Wannan na nuni da cewa, ba wata kasa da za ta iya tsira daga barazanar wannan annoba ta COVID-19, don kawai ta kare kan ta, ba tare da yin hadin gwiwa da sauran sassan duniya wajen ganin bayan cutar a matakin kasa da kasa ba.

A takaice dai, ba wata kasa da za ta samu cikakken tsaro daga COVID-19, har sai dukkanin duniya ta samu tsaro daga cutar. Lallai wannan aiki ne mai wahalar gaske amma kuma ya zama tilas!

Idan an kalli wannan batu da idon basira, ana iya ganin wasu kalubalen dake gaban bil Adama masu kama da hakan, kamar sauyin yanayi, da karewar albarkatun da bil Adama ke bukata, da matsalolin tsaro, da zaman lafiya, da rashin daidaito tsakanin sassan duniya, wadanda dukkanin su kalubaloli ne da ya dace bil Adama ya yi hadin gwiwar shawo kan su cikin hadin gwiwa.

Cutar COVID-19 ta jaddada wannan bukata, ta kuma zamo darasi na irin bukatar da daukacin bil Adama ke wa juna, wajen daukar matakan magance matsaloli tare, don a gudu tare a tsira tare. (Saminu)