logo

HAUSA

Ba a fafe gora ranar tafiya

2020-12-29 16:39:17 CRI

Ba a fafe gora ranar tafiya_fororder_A

A baya bayan nan ne aka gudanar da ranar shiryawa tunkarar annoba ta duniya da majalsiar Dinkin Duniya ta ware. Manyan annoba kamar cututtuka masu yaduwa, irinsu COVID-19 da Ebola da sauransu, na mummunan tasiri ga harkokin rayuwa da ci gaban tattalin arziki cikin lokaci mai tsawo. Irin wadannan cututtuka kan kawo matsi kan tsarukan kiwon lafiya da tsaiko kan harkokin samar da kayayyakin bukatu da jefa rayuwar bil adama cikin mawuyacin hali, baya ga tsananta yanayi a kasashe da yankuna matalauta da kuma mutane masu rauni.

Wannan rana a bana, ta zo a lokacin da ya dace na kara tunatar da cewa, akwai bukatar gaggauta samar da ingantattu tsarukan kiwon lafiya masu juriya, wadanda za su isa ga dukkanin mutane dake da rauni ko marasa rauni.

A yayin da aka rasa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, illar da annoba za ta yi a nan gaba ka iya fin wadanda aka gani a baya ta fuskar tsanani da karfi. Akwai matukar bukatar kara wayar da kan al’umma da musayar bayanai da dabaru da ilimin kimiyya da ilimi mai inganci, tun daga matakan kananan hukumomi, zuwa jihohi da kasa da kasa da yankuna da ma duniya baki daya, a matsayin hanya mafi nagarta ta kandagarki da tunkarar annoba.

Ba a fafe gora ranar tafiya_fororder_B

Hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya zai taka muhimmiyar rawa wajen shiryawa tunkarar annoba. Ya kamata a fahimci karfin hadin gwiwa da taimakekeniya tsakanin daidaikun mutane da al’ummomi a dukkan matakan tunkarar annoba, tun kafin isowarta.

Har ila yau, ya kamata kowa da kowa daga kan daidaikun jama’a zuwa gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki, su san hakkin da ya rataya a wuyansu da kuma rawar da su taka wajen kawar da aukuwar annoba, ko daukar matakan kandagarki da na dakile ta.

Barkewar annobar COVID-19 a bana, ya nunawa duniya cewa, babu wani wuri da zai tsira muddun wani bangare na fuskantar annoba ko kalubale, kana ya nuna cewa kowa yana da rawar takawa wajen kare ta’azzarar cutar. Sannan ya nunawa gwamnatocin da ba su mayar da hankali kan inganta rayuwar al’ummominsu ba, illar dake tattare da rashin yin haka. Don haka, akwai bukatar kara zage damtse da shirin ko ta kwana, don rage irin illolin da ake fuskanta a yanzu, maimakon ta’azararsu, idan duniya ta kuma fuskantar wata annobar mai kama da wadda take fuskanta a yanzu. (Fa'iza Mustapha)