logo

HAUSA

Mai da jama’a a gaban kome shi ne alamar kasar Sin a shekarar 2020

2020-12-26 16:32:18 CRI

Mai da jama’a a gaban kome shi ne alamar kasar Sin a shekarar 2020_fororder_微信图片_20201226163134

Mutane fiye da miliyan 78 sun kamu da cutar COVID-19 yayin da wasu miliyan 1.73 sun mutu sakamakon wannan cutar. A lokacin da ake fama da annobar, an sake nazartar dangantakar dake tsakanin daidakon mutane da al’umma da kuma tsakanin jama’a da kasarsu.

A matsayinta na kasa ta farko a duniya da ta fara ganin tasirin wannan annoba, kasar Sin ta kasance a kan gaba wajen dakile cutar da komawa bakin aiki har ma ta kyautata halin da ake ciki daga samun dan koma baya zuwa samun farfadowar tattalin arzikinta, ban da wannan kuma, ta cimma nasarar kawar da kangin talauci a duk fadin kasar kamar yadda aka tsara. Shin me ya sa Sin ta iya samun irin wadannan nasarori? Manazarta za su samu amsoshi bisa nazartar karfin tattalin arzikin kasar, da tsarin mulkin kasar, da manufofin da gwamnati ke dauka da sauransu. Daga cikinsu, abu mafi muhimmanci shi ne jam’iyyar JKS ta kasar Sin ta kan mai da moriyar jama’a a gaban kome, da ma dogaro da jama’a don tinkarar duk wasu wahalhalu. Matakin da ya zama alamar kasar Sin a wannan shekara.

Babban jami’in WHO da ya jagoranci wata tawaga da ta ziyarci kasar Sin Bruce Aylward ya bayyana cewa, Sin tana da dabara mai kyau wajen warkar da wadanda suka kamu da cutar, Sin ta kudiri aniya kuma ta zuba jari da dama a wannan fanni. Ya ce, “Sin ta yi amfani da duk wani abin da take da shi don ceton rayukan jama’arta”. Jaridar Nezavissimaia Gazeta ta kasar Rasha ta ba da labari cewa, Sin ta dora muhimmanci matuka kan rayuwar jama’a duk da cewa, ceton dukkan mutane na bukatar kashe makuden kudi.

Dadin dadawa, gwamnatin kasar Sin na yi iyakacin kokari raya tattalin arziki da al’umma yayin da take kokarin yakar cutar, don jagoranci jama’arta da su fita daga mawuyancin hali.

Abin lura shi ne, kasar Sin ta mai da aikin samar da guraben ayyukan yi da tabbatar da zaman rayuwar jama’a a gaban kome. Inda ta dauki jerin manufofin kudi da rage haraji don taimakawa kamfanoni, da ma tallafawa kamfanoni dake fuskantar mawuyancin hali, da wadanda ba su da isashen kudin shiga. Duk wadannan kokarin da Sin take yi ya samu nasara, ganin yadda yanayin karuwar GDPn kasar a watanni 9 na farkon bana ya kyautatu sosai.

Duk da cewa ana fuskantar babban kalubale a bana, Sin ta cika alkawarin da ta yi na kawar da talauci kafin karshen shekarar 2020.

Abubuwan da suka faru a kasar Sin a cikin shekarar 2020, ya shaidawa masu nazarin al’amuran duniya na kasashe daban daban cewa, nacewa ga kokarin tabbatar da hakkin jama’a na rayuwa da raya kansu shi ne alkawarin da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta dauka. Kuma shi ne alamar tsarin siyasar kasar Sin. (Amina Xu)