logo

HAUSA

Matakin mallake allurar rigakafin COVID-19 da kasashen yamma ke dauka na lahanta hadin kan kasa da kasa na yakar cutar

2020-12-25 21:25:50 CRI

Matakin mallake allurar rigakafin COVID-19 da kasashen yamma ke dauka na lahanta hadin kan kasa da kasa na yakar cutar_fororder_微信图片_20201225210414

Kwanan baya, kamfanin watsa labarai na ABC ya wallafa wani bayani mai taken “Kasashe masu wadata na kokarin mallakar allurar rigakafin COVID-19, amma kasashe marasa karfi ba sa iya samu”. Hakan dai na nufin yawan alluran da kasashe masu wadata kamar su Amurka, da Canada, da Birtaniya da sauransu suke mallaka, zai zarce yawan jama’arsu.

Bisa rahoton da kungiyar hadakar alluran rigakafin jama’a ta PVA ta gabatar a farkon wannan wata, ko da yake yawan jama’a na kasashe masu wadata ya kai kashi 14% bisa daukacin yawan jama’ar duniya, a hannu guda, yawan alluran da suke mallaka ya kai fiye da rabi.

A sa’i daya kuma, a kasashe marasa karfi 67 ciki hadda Kenya, da Myanmar da Najeriya, kashi 10% ne kadai na jama’ar su za su iya samun allurar kafin nan da karshen shekarar badi.

A nasa tsokaci, darektan cibiyar kandagarkin annoba ta Afrika John Nkengasong, ya ce kasashe masu wadata, har kullum su kan yi biris da bukatun Afrika a fannin magunguna da alluran rigakafi.

Sai dai a matsayinta na kasa dake sahun gaba da duniya wajen fitar da alluran, kasar Sin na kokarin rarraba alluran cikin daidaito, musamman ma bisa kokarin samarwa kasashe masu tasowa allurai masu araha, duk da cewa “Hannu daya ba ya dauka jinka”, yakar wannan mummunar cuta na bukatar hadin kan kasa da kasa, musamman ma kasashe masu wadata, su yi hangen nesa, da ma sauke nauyin dake wuyan su. (Amina Xu)