logo

HAUSA

Ko Da Gaske Ne Ana Tilastawa Mutane Aiki A Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin?

2020-12-22 21:10:34 CRI

Ko Da Gaske Ne Ana Tilastawa Mutane Aiki A Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin?

“Mun samu aikin yi, sa’an nan za mu samu kudi, da kwarewar aiki, ta yadda za mu iya kyautata zaman rayuwarmu. Ko hakan na bukatar a tilasta mana?” A jiya Litinin, Shieli Memetmin, wanda ke zaune a yankin Hotan na jihar Xinjiang ta kasar Sin, ya amsa wata tambayar da aka yi masa, dangane da batun “tilastawa mutane aiki a jihar Xinjiang”, a wajen wani taron manema labarun da aka kira bisa wasu batutuwa masu alaka da jihar.

Da farkon bana, wasu mutane masu kin jinin kasar Sin na kasar Amurka da wasu kasashe dake yammacin duniya, sun fake da batun kare hakkin dan Adam, inda suke kokarin yayata maganar cewa “Ana tilastawa mutane yin aiki” a jihar Xinjiang, gami da kaddamar da wasu dokoki don saka takunkumi kan wasu jami’ai, da hukumomi, da kamfanonin jihar. Dalilin da ya sa suke yin hakan shi ne, domin neman tabbatar da moriyarsu a fannin tattalin arziki, gami da yunkurin haddasa tsamin dangantaka tsakanin al’ummonin kasar Sin, da shafawa kasar Sin bakin fenti, don hana ta samun ci gaba.

Hakika, maganar nan ta kasancewar “tilastawa mutane aiki” a Xinjiang, wani masani dan asalin kasar Jamus mai suna Adrian Zenz ne ya kirkiro ta, tare da cibiyar nazarin manyan tsare-tsare na kasar Australiya (ASPI), duk da cewa ba su taba gabatar da hakikanan shaidu ba.

A watan Maris na bana, wani shafin yanar gizo ta Intanet mai suna “The Grayzone” ya taba karyata maganar, inda ya ce wasu mutane masu kin jinin kasar Sin na kasashen Amurka da Australiya ne suka tsara wannan aiki na yada jita-jita, don neman ta da rikici a duniya, tare da samun riba daga ciki.

Ta haka za mu iya ganin cewa, maganar “tilastawa mutane aiki” jita-jita ce kawai, wadda ake kokarin yada ta, don neman keta hakkin al’ummomin jihar Xinjiang na kasar Sin, na samun zaman rayuwa mai kyau ta hanyar kokarin aiki. Suna neman hana jihar Xinjiang samun ci gaba, ta yadda za su iya ci gaba da yin amfani da wurin don ta da rikici a kasar Sin. Gaskiya wadannan mutane ba su da kirki ko kadan.

Hakika gwamnatin kasar Sin, a nata bangare, tana ta kokarin samar da karin guraben aikin yi ga jama’ar kasar, don tabbatar da ingancin zaman rayuwarsu. A ganinta, batun nan ya shafi aikin raya tattalin arziki a jihar, da tabbatar da kwanciyar hankali, da moriyar al’ummu daban daban na jihar.

A watan Satumba da na Oktoban bana, an taba gabatar da takardar bayani kan yadda ake samar da guraben aikin yi a Xinjiang, da rahoton yadda ’yan wasu kabilu suke samun ayyuka a jihar. Bisa nazarin da aka yi, da hakikanan shaidun da aka samu, ana iya tabbatar da cewa, babu batun “tilastawa mutane aiki” a jihar Xinjiang.

Kana bisa wasu managartan manufofin da gwamnati ta samar, ’yan wasu kabilun dake jihar Xinjiang, suna neman aiki ne bisa son ransu kuma cikin ’yanci. Tun daga shekarar 2014 har zuwa yanzu, wasu mutane dubu 117 na jihar sun taba aiki a wurare daban daban na kasar Sin. (Bello Wang)

Bello