logo

HAUSA

Shure-shure baya hana mutuwa

2020-12-22 17:08:26 CRI

Shure-shure baya hana mutuwa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya mayar da martani dangane da jita-jitar da ake ci gaba da yadawa, inda wani rahoto na baya-bayan na kamfanin dillancin labarai na Reuters ke cewa, wai wata kungiyar leken asiri ta kasar Sin ta yi kutse a hedkwatar Tarayyar Afrika AU, har wata kafar watsa labarai ta kasar Faransa mai suna Le Monde, ta ba da rahoto kan yadda wai kasar Sin take leken asiri kan hedkwatar AUn shekaru biyu da suka gabata.

Dangantakar Sin ta Afrika ta kasance ta moriyar juna ce bisa gaskiya da mutunci da kuma adalci. Wadanda kuma wani bangare ne na ka’idar kulla dangantaka da kasar Sin. Kasar Sin ta kan yi adawa da duk wani mataki ko yunkurin tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta ko na kasashe kawayenta. Abu ne da aka riga aka sani cewa, kasar Sin ba ta tsoma baki cikin batutuwan cikin gidan kasashe, haka zalika ba ta gindaya sharadin siyasa a tsarin huldarta. Don haka abun tambaya shi ne, shin amfanin me leken asiri zai mata, bayan kuma tana da wakilai da jakadu a tarayyar? Cikin shekaru da dama, an ga yadda dangantakar bangarorin biyu ke ci gaba da habaka maimakon tabarbarewa kamar yadda masu yada jita-jita ke fata. Wannan kadai ya isa ya nuna cewa, kasashen Afrika sun aminta da kasar Sin, kuma akwai gaskiya da sahihanci cikin dangantakarsu.

Wadannan jita-jita alamu ne na kokarin wasu na lalata kyakkyawar dangantakar da aka kulla bisa nagartaccen tubali shekara da shekaru. Hakar masu yada jita-jita ba za ta cimma ruwa ba. Sanin kowa ne cewa kasashen yammacin duniya na kishin irin dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika a yanzu. Bayan a baya sun ma fi Sin din samun dama, wato a lokacin da suka yi mulkin mallaka, amma ba su tabuka komai ba, illa azurta kansu, sai kuma yanzu da suka ga yadda Sin ke namijin kokari wajen tabbatar da kasashen Afrika sun samu ci gaba, kuma ake samun moriyar juna a tsakaninsu, sai kuma suke da na sani, wanda Hausawa kan ce “keya ce”. Haka kuma, shure-shure baya hana mutuwa. Lokaci ya riga ya kwace musu, domin kasashen Afrika sun riga sun farga kuma sun gane mai taimakonsu da son ci gabansu, wato an yi walkiya, sun ga gari. (Faeza Mustapha)