logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Samar Da Wani Yanayi Na Tabbas A Duniya

2020-12-20 20:11:52 CRI

Kasar Sin Ta Samar Da Wani Yanayi Na Tabbas A Duniya

Taron kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin game da aikin tattalin arziki da aka rufe a kwanakin baya ya nuna wani sako mai muhimmanci, wato za a tabbatar da wani yanayi na zaman karko a cikin manufar kasar Sin ta fuskar raya tattalin arziki a shekarar 2021, inda ake neman nuna hangen nesa, don tabbatar da samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa, gami da magance haddura.

Ko da yake tattalin arzikin kasar Sin ya riga ya koma kan hanyar samun farfadowa, amma har yanzu akwai sauran rina a kaba, inda ba a samu farfado da wasu ayyuka da sana’o’i ba tukuna, kana dole a yi kandagarki game da wasu haddura wanda yaduwar annobar COVID-19 ka iya haddasawa. Saboda haka ana kokarin kiyaye dorewar manufar tattalin arzikin kasar, ta yadda tattalin arzikin zai samu farfadowa sosai a shekara mai zuwa.

Hakika wannan yanayi na samun tabbaci ya riga ya zama wani abun da kasashe daban daban suke bukata, bisa la’akari da yadda ake jin radadin yaduwar cutar COVID-19. Kasancewarsa tattalin arziki mafi girma na 2 a duniya, yadda tattalin arizkin Sin ke samun farfadowa wani abu ne mai kyau da ke iya taimakawa kawar da damuwar samun lalacewar tattalin arzikin duniya. A kwanakin nan, kasar Sin ta sanar da alkaluman bangaren tattalin arizkin kasar na watannin Janairu zuwa Nuwamban bana, wadanda suka nuna yadda ake samun karuwa a fannonin masana’antu, da aikin sayar da kayayyaki, da bangaren zuba jari, da makamantansu. Dangane da batun, wata kafar yada labarai ta kasar Jamus ta ce, hakan tamkar wata kyauta ce da kasar Sin ta ba tattalin arzikin duniya. Saboda yadda ake samun karuwar tattalin arziki a kasar Sin, ya samar da wani yanayi na tabbas, wanda da wuya ne ake samun damar ganinsa a halin yanzu. Lamarin ya hada da yadda ake kokarin samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasashe daban daban, shi ya sa ake sa ran ganin farfadowar tattalin arzikin duniya a shekarar 2021.

Ta la’akari da matsayin kasar Sin na “babbar ma’aikatar dake samar da kayayyaki kala-kala ga kasashe daban daban”, yadda ake samun farfadowar tattalin arziki a kasar Sin, yana da muhimmanci matuka ga yunkurin daidaita bangarorin masana’antu masu samar da kayayyaki wadanda suka ji raunuka sosai sakamakon yaduwar annobar COVID-19. A watan Nuwamban da ya gabata, darajar kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen waje ta karu da kashi 21.1%, wanda ya zama mafi yawa tun bayan watan Fabrairun shekarar 2018. Ta wannan za mu iya ganin cewa, ma’aikatun kasar Sin suna kokarin samar da kayayyaki don biyan bukatun jama’ar kasashe daban daban.

Wadannan alkaluma sun karyata zancen wasu ‘yan siyasar kasashen yammacin duniya, na “ katse hulda da kasar Sin”. Martin Wolf, shi ne babban mai wallafa sharhi a fannin tattalin arizki na jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya. Ya ce, har zuwa yanzu kasar Sin ta ci gaba da zama daya daga cikin wurare inda masana’antu na da matukar karfi.

Kana yadda kasar Sin take haifar da yanayi na tabbas a duniya bai tsaya a bangaren masana’antu kawai ba. Saboda yanzu haka mutanen duniya suna maida hankali sosai kan kasuwannin kasar Sin, wadanda suke neman kara bude kofofinsu ta wata hanya mafi inganci. Ko da yake jarin da ake zuba wa sauran kasashe na kai tsaye ya ragu sosai a duniyarmu, amma kasar Sin na ci gaba da samun karin kudaden jarin da ake kokarin zuba wa kasuwanninta, har ma adadin jarin da ta samu tsakanin watan Janairu zuwa na Nuwamban bana ya karu da kashi 6.3%, idan an kwatanta da na bara. Wannan batu ya nuna yadda masu zuba jari na kasashe daban daban suke da cikakken imani kan kasuwannin kasar Sin.

Hakika don neman raya tattalin arzikinta, kasar Sin tana bukatar sauran kasashe, yayin da farfadowar tattalin arzikin duniya shima na matukar bukatar samun gudunmowa daga kasar Sin. Yadda ake samun farfadowar tattalin arziki a kasar Sin ba abu ne mai sauki ba. Saboda haka, kasar tana taka tsan-tsan a fannin gudanar da harkokin tattalin arziki, ta yadda take neman kwantar da hankalin jama’ar kasar, gami da karfafa wa jama’ar kasashe daban daban gwiwarsu. (Bello Wang)

Bello