logo

HAUSA

Ana gudanar da sabon tsarin raya kasar Sin yadda ya kamata

2020-12-19 16:30:27 CRI

Ana gudanar da sabon tsarin raya kasar Sin yadda ya kamata

An kira taron tattauna aikin raya tattalin arziki na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na shekara-shekara a nan birnin Beijing tsakanin ranekun 16 zuwa 18 ga wannan wata, inda aka takaita aikin raya tattalin arzikin kasar a bana, sannan aka yi nazarin yanayin tattalin arziki da ake ciki yanzu. Baya ga haka, an tsara shirin raya tattalin arziki a kasar a shekarar 2021 dake tafe, tare kuma da gabatar da wasu bukatu kamar; kara mai da hankali kan sabon tsarin raya kasa a shekara mai zuwa, da kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki bisa matakin sauri mafi dacewa. Taron da ya ba da jagoranci kan aikin raya tattalin arzikin kasar a shekarar 2021, tare kuma da samar da damammaki ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Taron tattauna aikin raya tattalin arziki na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na wannan shekara, ya fi jan hankalin al’ummun kasa da kasa, saboda ana iya fahimtar manufofin tattalin arzikin da gwamnatin kasar Sin ta tsara bisa manyan tsare-tsare, kuma 2021, ita ce shekara ta farko da za a fara gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14. A don haka taron yana da ma’ana ta musamman, kana bisa matsayinta na kasa daya kacal da ta cimma burin karuwar tattalin arziki a fadin duniya yayin da ake fama da matsalar yaduwar annobar numfashi ta COVID-19, hukumomin kasa da kasa sun jinjinawa kokarin da kasar Sin take yi, kuma suna fatan za ta kara taka rawa kan ci gaban tattalin arzikin duniya.

Hakika sau da dama, kasar Sin ta taba jaddada cewa, makasudin aiwatar da sabon tsarin raya kasa shi ne, kara habaka cudanyar dake kasuwar cikin gidan kasar da kuma cudanyar dake tsakanin kasuwarta da kasuwannin kasa da kasa.

Kana ma’anar habaka bukatun gida, ita ce kara karfin kasuwar kasar Sin har ta kasance kasuwar kasa da kasa, ta hanyar tsara namufofin da suka dace da sayayya da adana kudi da zuba jari da sauransu.

A sa’i daya kuma, an jaddada a yayin taron cewa, ya dace a kara karfafa daidaita manufofin kasa da kasa da aka tsara bisa manyan tsare-tsare, kuma a samar da muhallin kasuwanci mai inganci bisa doka, kana a yi la’akari da batun shiga yarjejeniyar cinikayya cikin ‘yanci ta CPTPP wato Comprehensive and Progressive Agreement for Trans-Pacific Partnership.

Matakan da kasar Sin ta dauka sun nuna cewa, kasar tana kara bude kofa ga ketare daga dukkan fannoni bisa tsarin da ta tanadi.(Jamila)