logo

HAUSA

Ruhin binciken duniyar wata na kasar Sin zai zaburar da Sinawa wajen kara ba da gundumawa ga ci gaban Bil Adama

2020-12-18 10:37:06 CRI

Ruhin binciken duniyar wata na kasar Sin zai zaburar da Sinawa wajen kara ba da gundumawa ga ci gaban Bil Adama

Da safiyar jiya Alhamis ne na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5 ta dawo doron kasa tare da samfuran da ta debo. Ke nan Bil Adama ya sake samun samfuran duniyar wata bayan tsawon shekaru 44, matakin da ya shaida sabon ci gaban da kasar Sin ta samu ta fuskar nazarin sararin samaniya.

A wannan rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya murnar ci gaban da aka samu, inda ya nanata wajibcin habaka ruhin da ake da shi a wannan aiki, wato dukufa kan cimma buri, da kokarin yin bincike, da kuma yin hadin kai wajen haye wahalhalu da yin hadin gwiwar samun moriyar juna. Ko shakka babu, irin wannan tunani zai karawa Sinawa kwarin gwiwa, wajen nazarin sararin samaniya da kara kawowa alheri ga dukkannin Bil Adama.

Na’urar Chang’e-1 ce ta kaddamar da aikin nazarin duniyar wata, kuma Chang’e-3 ta samu nasarar sauka a doron duniyar wata tare da motar bincike mai suna “Yutu”, inda yanzu kuma sashen dawowa na Chang’e-5 ya dawo da samfura da ya debo daga duniyar wata. ‘Ayyukan nazari masu matakai uku da Sin ta aiwatar, wato “Zagaya duniyar wata, da sauka a doronsa, da dawowa doron kasa”. Matakai ne da suka sa Sin ta zama kasa ta uku da ta dawowa da samfuran duniyar wata.

Kafar watsa labarai ta BBC ta nuna cewa, nasarar Chang’e-5, wata shaida ce game da karfin nazarin sararin samaniya dake kara inganta na kasar Sin.

Kimiyya da fasaha ba su da iyaka, kuma kasar Sin na yin hadin gwiwa da sauran kasashe a fannin nazarin sararin samaniya. Bisa labarin da aka bayar, hukumar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin, ta kulla yarjejeniyar hadin kai a wannan fanni, tare da hukumomin kasashen waje 44, da ma kungiyoyin kasa da kasa 4, kuma tana hadin kai da sauran kasashe kan aikin binciken duniyar wata da ta duniyar Mars.

Karkashin aikin bincike duniyar wata, Sin ta yi hadin kai da hukumar nazarin sararin samaniya ta Turai wato ESA, da Argentina, da Namibiya, da Pakistan, da sauran kasashe da kuma hukumomin kasa da kasa.

(Amina Xu)