logo

HAUSA

Yanayi ne ke bayyana aminiyar kwarai ko kishiyarta

2020-12-15 20:01:24 CRI

Yanayi ne ke bayyana aminiyar kwarai ko kishiyarta

Yanayi ne ke bayyana aminiyar kwarai ko kishiyarta

A wani bangare na kara karfafa dangantakar dake ci gaba da habaka tsakanin Sin da nahiyar Afrika ta kowacce fuska, a jiya Litinin, aka aza harsashin ginin hedkwatar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta nahiyar Afrika a birnin Addis Ababa na Habasha, aikin da kasar ta taimaka wajen aiwatarwa.

Annobar COVID-19 ta zo wa duniya a ba-za-ta, inda ta kara matsi da kalubale kan wasu matsaloli da dama can ake fama da su. Bisa la’akari da matsayinsu na kasashe maso tasowa, tun dama kasashen nahiyar na fama da matsala a fannonin ababen more rayuwa, ciki har da na kiwon lafiya, inda tsarukan kula da lafiyar al’umma suka gaza kai wa matakin ingancin takwarorinsu na sauran sassan duniya.

Yayin da wasu ke aiwatar da ra’ayin gaban kai da kokarin zama saniyar ware, yanzu lokaci ne da ya dace a kara inganta huldar kasa da kasa. Kamar yadda shugaban kasar Sin kan bayyana, dukkan bil adama na da makoma iri guda, kuma annobar COVID-19 ta kara gaskata hakan. Don haka, hada hannu domin a gudu tare a tsira tare, shi ne hanyar da ta fi dacewa ga ci gaban duniya.

Hadin gwiwar Sin da Afrika ya zama abun misali ga sauran sassan duniya. Domin shekaru da dama bayan kulla dangantaka a tsakaninsu, babu abun da take haifar face dimbin alfanu ga bangarorin biyu, lamarin dake kara aminci da girmama juna a tsakaninsu.

An ce a lokacin da ake cikin mawuyacin hali ake gane aminiya ko aboki na kwarai. Kamar yadda kasar Sin ke goyon baya da taimakawa kawayenta na nahiyar Afrika a wannan lokaci da suke fama da annobar COVID-19, haka su ma suka bata goyon bayan a lokacin da cutar take ganiyar yaduwa a kasar. Duk da cewa, annobar ta yi wa kasar Sin illa, hakan bai sa ta nade hannu taki taimakawa ba, maimakon haka, sai ta kara nuna kimarta ta hanyar kara taimakawa da bada tallafi. Baya ga tarin kayayyakin tunkarar annobar da kwararru da dabaru da ta turawa nahiyar, ta kara hobbasa, inda take kokarin gina hedkwatar cibiyar kandagarki da dakile cututtuka a nahiyar. Wannan ya nuna cewa lallai kasar Sin aminya ce ta kwarai, kuma abun dogaro. Lallai ya kamata kasashen Afrika su fahimci hakan, domin kara kyautata dangantakarsu da aminiya ta kwarai, wadda a kullum burinta shi ne, ta ga sun samu ci gaba cikin kwanciyar hankali da lumana, maimakon daukar ci gaban nasu a matsayin barazana. (Faeza Mustapha)