logo

HAUSA

Yaushe Morrison zai daina neman moriyar kashin kai game da batun sauyin yanayi?

2020-12-15 20:45:28 CRI

Yaushe Morrison zai daina neman moriyar kashin kai game da batun sauyin yanayi?

Kawo yanzu gobara na ci har tsawon watanni biyu a tsibirin Fraser na kasar Australia, a sanadin haka, tsuntsaye da dabbobi dake rayuwa a tsibirin sun tsere, kana itatuwa sun kone kurmus, duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake yi a kwanakin baya ya kashe tashin gorabar, amma ambaliyar ruwan da ruwan saman sun haifar ta sake jefa yankin bakin tekun dake gabashin kasar ta Australia cikin mawuyacin yanayi.

Dalilin da ya sa masifar gobara ta auku a yankin shi ne sauyin yanayi, haka kuma domin manufofin siyasar da gwamnatin kasar take aiwatarwa, an ga alamar a yayin taron kolin da aka kira kan batun, game da yadda za a dakile matsalar sauyin yanayi a ranar 13 ga watan, inda firayin ministan kasar ta Australia Scott Morrison bai samu damar gabatar da jawabi ba.

Jaridar The Guardian ta fitar da rahoto mai cewa, an samar da damar yin jawabi ne ga shugabannin kasashe wadanda suka tsara muradun rage fitar da hayaki mai tattare sinadarin carbon, a cikin shekaru goma masu zuwa, a bayyane an lura cewa, kasar Australia wadda ke kawo illa ga yunkurin dakile sauyin yanayi na kasa da kasa ba ta samu damar ba.

Kafin shekaru biyar da suka gataba, Australia ta taba yin alkawari a yayin taron dakile matsalar sauyin yanayin da aka kira a birnin Paris cewa, adadin hayaki mai tattare sinadarin carbon da kasar za ta fitar zuwa shekarar 2030 zai ragu da kaso 26 zuwa 28 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2005, amma hasashen da aka yi a karshen shekarar 2019 ya nuna cewa, kila ne adadin zai ragu da kaso 16 bisa dari ne kawai.

Har kullum Australia ba ta daukar matakin da ya dace kan batun dakile matsalar sauyin yanayi, inda ta kasance kasa mafi ci gaban masana’antu daya kacal, wadda ta ki sa hannu kan yarjejeniyar Kyoto, wato ban da kasar Amurka, daga baya duk da cewa ta daddale yarjejeniyar Paris, amma ba ta cika alkawari ba bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar.

Hakika dakile matsalar sauyin yanayi nauyi ne dake wuyan daukacin bil Adama, shi ma ya dace da babbar moriyar al’ummun kasar ta Australia, yanzu haka ba zai yiwu firayin ministan kasar Morrison ya boye ainihin yunkurinsa ba, wato ya yi biris da moriyar al’ummun kasarsa, amma ya yi kokarin kare moriyar rukunin siyasar dake goyon bayansa, ana ganin cewa, ba zai yiyu wanda ya kasa kula da gobarar daji a yanyin kasa, zai bautawa al’ummun kasarsa ba. Abun tambaya a nan shi ne, yaushe ne zai daina neman cimma moriyar kashin kansa kan batun sauyin yanayi?  (Jamila)