logo

HAUSA

Kalaman Xi a taron sauyin yanayi ya baiwa duniya kwarin gwiwa

2020-12-14 17:25:37 CRI

Kalaman Xi a taron sauyin yanayi ya baiwa duniya kwarin gwiwa

Masu hikimar magana na cewa, “hannu daya baya daukar jinka”. Batun sauyin yanayi al’amari ne dake shafar makomar dukkan bil adama, kama daga yanayin ingancin abincinsu, iskar da suke shaka, har ma da yanayin muhallin da halittu ke rayuwa cikinsa. Ga masu bibiyar harkokin dake wakana na yau da kullum sun kwana da sanin cewa a shekaru biyar da suka gabata, an zartas da yarjejeniyar Paris a yayin babban taron MDD da aka kira domin tattauna batun dake shafar matsalar sauyin yanayi a birnin Paris na kasar Faransa, inda aka tsara shirin tinkarar matsalar sauyin yanayi bayan shekarar 2020, sai dai abin takaici ne yadda gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjejeniyar, bisa dalilai na moriyar kashin kanta, koda yake, matakin ya janyo mata suka daga kasashen duniya bisa yin rikon sakainar kashi da wannan muhimmin bangare. Sai dai kuma, a nata bangaren, kasar Sin ta sha jaddada aniyarta na cigaba da yin cudanya da kasashen duniya wajen tinkarar dukkan batutuwan dake shafar makomar kasa da kasa ciki har da batun na sauyin yanayin domin a gudu tare a tsira tare a maimakon fifita bukatu da moriyar kashin kai. A bisa ga wannan dalili kalaman da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya furka cikin jawabin da ya gabatar a taron kolin sauyin yanayin yayi matukar tasiri wajen baiwa kasashen duniya kwarin gwiwa da sa kaimi garesu da su kara himma da sanya kokari domin dakile matsalar. Kamar yadda wani masani kan yanayi da muhalli, Magdy Allam ya ce, jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a taron kolin kasa da kasa da aka kira kan sauyin yanayi ya samar da kwarin gwiwa da hikima ga dabarun duniya na tinkarar sauyin yanayi tare da nuna kudurin kasar Sin na yaki da sauyin yanayi tare da al’ummomin duniya. Da yake jawabi ga taron ta kafar bidiyo, shugaba Xi ya bukaci dukkan bangarori su hada kai tare da samar da sabbin nasarorin moriyar juna a fannin tinkarar sauyin yanayi. A cewar masanin, jawabin na shugaban kasar Sin ya nuna kudurin kasar na sauya kanta zuwa kasa mai kyautata muhalli da inganta muradun ci gaba masu dorewa na duniya. Ya kara da cewa, alkawurran da shugaban kasar Sin ya sanar sun nuna cewa, lallai kasar Sin ta damu da batun sauyin yanayi kuma za ta dauki sahihan matakai domin tinkarar batun yadda ya kamata. Shi ma wani mai sharhi kan huldar kasa da kasa na kasar Kenya Cavince Adhere, yana da irin wannan ra’ayi inda ya nuna cewa, shawarwarin shugaba Xi sun samar da wani kyakkyawan yanayi na kara hada hannu wajen tinkarar sauyin yanayi a duniya. Har kullum, babban burin Sin bai wuce hada karfi da karfe tsakanin kasa da kasa domin samar da duniya mai cike da zaman lafiya da wadata ba. (Ahmad Fagam)