logo

HAUSA

Shin Twitter ba shi da hankali ne?

2020-12-14 20:49:25 CRI

Shin Twitter ba shi da hankali ne?

Jiya 13 ga watan Disamba, rana ce ta nuna juyayi ga wadanda suka rasu yayin kisan gillar da aka yi a birnin Nanjing, inda daukacin al’ummun kasar Sin suka yi bakin ciki matuka ga ‘yan uwansu sama da dubu 300 wadanda suka mutu sakamakon kashe-kashen da maharan Japanawa suka yi musu shekaru 83 da suka gabata, tare kuma da nuna fatansu na koyon darasi daga tarihi da darajanta zaman lafiya, amma kowa ya ga abun bacin rai da ya faru a dandalin sada zumunta na Twitter, inda aka goge hotunan tarihi da hoton bidiyon kisan gillar da ya faru a Nanjing da wasu masu shiga dandalin suka yi, bisa dalilin hotuna marasa dadin gani, a sakamakon haka, an ga wasu tsokacin karya da masu sassaucin ra’ayin kasar Japan suka gabatar a dandalin.

Ma’auni iri biyu da dandalin Twitter ke amfani da shi, ya sake nuna ainihin ma’anar ‘yancin bayyana ra’ayi na wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma, kuma ya sake shaida cewa, wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma, suna siyasantar da abubuwan da suka gabata.

Kamar yadda aka sani, kisan gillar Nanjing da ya faru a shekarar 1937 laifi ne da kotun sojan kasa da kasa mai kula da yankin gabashin Asiya ta tabbatar, hotuna da bidiyon da dandalin Twitter ya goge hotuna ne da suka shaida abubuwan da suka faru a tarihi, wadanda suka samu amincewa daga al’ummun kasa da kasa, yanzu haka Twitter yana yin amfani da ma’auni iri biyu kan wannan babban laifin da ya keta wayewar kan bil Adama, amma ko ya san me yake yi? Ko kuma hankalinsa ne ya gushe?

Hakika wannan ba shi ne karo na farko da Twitter ya yi haka ba, misali yayin da aka gamu da matsalar gyara doka a yankin Hong Kong a shekarar 2019, shahararrun dandalolin kasar Amurka kamar su Twitter da Facebook da sauransu sun taba rufe adireshin masu amfani da dandalin sama da dubu daya bisa dalilin wai suna ba da labaran karya ko suna samun goyon bayan gwamnatin kasar Sin, amma hakika suna gabatar da labarai na hakika da suka faru a yankin Hong Kong, a maimaikon haka, dandalin Twitter ya amince a gabatar da rahotannin da suke shafa wa ‘yan sandan Hong Kong ko gwamnatin kasar Sin bakin fenti.

Daga hakikanan matakan da dandalin sada zumunta na Twitter ya dauka, an lura cewa, yana dogaro ne kan rukunin da ya samar masa kudi da moriyar kasar Amurka, ana iya cewa, Twitter dandalin siyasa ne wanda ke kare muradun kasar ta Amurka,(Jamila)