logo

HAUSA

Sin ta cika alkawarin ingiza yunkurin dakile matsalar sauyin yanayi

2020-12-13 17:20:45 CRI

Sin ta cika alkawarin ingiza yunkurin dakile matsalar sauyin yanayi

A yammacin jiya Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a wajen taron kolin da aka kira domin dakile matsalar sauyin yanayi ta kafar bidiyo, inda ya gabatar da shawarwari guda uku a bangaren, tare kuma da sanar da wasu sabbin matakan da kasarsa za ta dauka domin rage fitar da hayaki mai tattare da sinadarin carbon nan da shekarar 2030, lamarin da ya ba da jagoranci kan aikin da ake yi a bangaren dakile matsalar sauyin yanayi a fadin duniya.

Kafin shekaru biyar da suka gabata, an zartas da yarjejeniyar Paris a yayin babban taron MDD da aka kira domin tattauna batun dake shafar matsalar sauyin yanayi a birnin Paris na kasar Faransa, inda aka tsara shirin tinkarar matsalar sauyin yanayi bayan shekarar 2020, amma yanzu gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjejeniyar, bisa dalilin moriyar kashin kanta, matakin da ya kawo cikas ga kokarin da kasashen duniya suke yi a bangaren, a sanadin haka, ya dace kasashen duniya su kara sanya kokari domin dakile matsalar.

Yayin taron kolin jiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda uku, kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su kara karfafa hada kan dake tsakaninsu domin kafa sabon yanayin moriyar juna wajen dakile matsalar sauyin yanayi, kuma su kara sanya kokari domin kafa sabon tsarin dakile matsalar sauyin yanayi, kana su kara karfafa imanin al’ummunsu domin nacewa kan sabuwar manufar dakile matsalar sauyin yanayi ta hanyar farfado da tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba, an lura cewa, shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar sun nuna nauyin da wani shugaban babbar kasa ke sauka bisa wuyansa kan makomar bil Adama.

A ciki, shawarar nacewa kan ka’idar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban ta fi muhimmanci, dalilin da ya sa haka shi ne, kiyaye muhallin doron duniya, yana shafar daukacin kasashen duniya, bai kamata ba a gudanar da harkokin da abin ya shafa bisa ka’idar nuna bangaranci, kana bai dace ba ya kasance kasashe kalilan ne kawai zasu yi kokari, ya zama wajibi kasashen duniya su gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu, a sa’i daya, bisa dalilin bambancin yanayin kasa da karfin kasa, ya kamata kasashe masu ci gaba su sauke karin nauyi, su samar da tallafin kudade da fasahohi ga kasashe masu tasowa, ta yadda za a yi nasarar dakile matsalar sauyin yanayi daga dukkan fannoni.

Hakika, daukar matakai ya fi yawan maganganu muhimmanci, har kullum kasar Sin tana daukar matakan da suka dace a kan lokaci, yayin taron jiya, shugaba Xi ya sanar da cewa, adadin hayaki mai tattare da sinadarin carbon na kasar Sin ya ragu da kaso 65 bisa dari idan an kwatanta da shekarar 2005, kuma adadin makamashin da ba na mai ko kwal ko gas ba da kasar Sin zata yi amfani da su zai kai kaso 25 bisa dari nan da shekarar 2030.

Duk wadannan sabbin matakai sun nunawa kasashen duniya cewa, kasar Sin tana yin kokarin dakile matsalar sauyin yanayi ta hanyar daukar hakikanan matakai bisa shirin da aka tsara.(Jamila)