logo

HAUSA

Me ya sa kasar Amurka ke fuskantar rabuwa

2020-12-10 20:48:41 CRI

Me ya sa kasar Amurka ke fuskantar rabuwa

"Abin da ya bari a wa'adin mulkinsa shi ne, wata kasar Amurka dake cikin kufai—wato ba a taba raba kan ta kamar haka ba tun lokacin Yakin Basasa." A watan Yunin wannan shekarar, jaridar Le Figaro ta kasar Faransa, ta buga wani sharhi kai tsaye, inda aka nuna cewa, manufofin shugaban Amurka sun kawo "Barkewar Amurka". Bayan watanni shida, musamman hargitsin da aka tayar a zaben Amurka, ya tabbatar da cewa wannan hukuncin ba karin gishiri ba ne.

Abu na farko shi ne, gibin dake karuwa tsakanin attajirai da talakawa. A cewar wani rahoto da cibiyar nazarin manufofin Amurka (IPS) ta fitar a karshen Nuwamba, tun daga watan Maris, lokacin barkewar annobar COVID-19 a Amurka har zuwa ranar 24 ga watan Nuwamba, arzikin attajirai 650 a Amurka ya karu da sama da dala tiriliyan 1, adadin da ya kai kusan dala tiriliyan 4. Akasin haka, iyalai na Amurkawa na cikin halin rashin kudi, sakamakon sakaci da aiki da gwamnatin kasar ke yi wajen dakile cutar, har ma yawan marasa aikin yi ya wuce miliyan goma.

Me ya sa kasar Amurka ke fuskantar rabuwa

A hakika dai, tun daga habakar salon kasuwa na jari hujja a farkon 1980s, tsarin jari hujja na Amurka ya samu saurin ci gaba, kuma yana bin riba a duk duniya. Tsarin tattalin arzikin kasar ma ya fara canzawa, kuma arziki da maganganun siyasa suna kara kasancewa a hannun attajirai da manyan masu kudin shiga.

Idan babu wani canji a yanayin siyasar cikin gida na Amurka, to, rikice-rikicen da ke cikin kasar za su kasance ba a warware su ba. Ya kamata gwamnati mai zuwa ta Amurka, ta saurari shawarar jaridar Le Figaro: Sharadi na farko na babbar kasa shi ne hadin kan kasar, kuma babban abin da aka sanya a gaba shi ne "sake sanya Amurka ta zama wata haddadiyar kasa." (Bilkisu)