logo

HAUSA

Hangen dala ba shi ne shiga birni ba

2020-12-09 17:54:56 CRI

Hangen dala ba shi ne shiga birni ba

A yayin da duniya ke fama da annobar COVID-19. A hannu guda kuma wasu kamfanonin harhada magunguna na kokarin fito da alluran riga kafin cutar da suka samar.

Ita ma kasar Sin kamar sauran kasashe da suka dukufa wajen nazari da samar da riga kafin annobar, ta yi nisa a fannin nazari da samar da riga kafin annobar COVID-19 masu inganci, inda ta yi alkawari cewa, da zarar ta yi nasarar samar da wadannan riga kafi, to zai zama kayan al’ummar duniya, kuma kasashe masu tasowa musamman kasashen Afirka ne za su fara amfana.

Sai dai, duk da irin wannan ci gaba da aka samu a fannin samar da riga kafin annobar da ake ganin da zarar an fara amfani da ita, za ta taimaka wajen rage irin illar da annobar ta yiwa sassa daban-daban na duniya, babban sakataren hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya damu, sabo yadda wasu mutane ke ganin cewa, allurar rigakafin za ta kawo karshen yaduwar annobar, amma, gaskiyar magana ita ce, annobar na ci gaba da yaduwa a wasu sassan duniya cikin sauri, lamarin da ya kara cusa ma’aikatan lafiya cikin matsi.

Masana lafiya sun sha bayyana cewa, yaki da cutar COVID-19 aiki ne mai wahala dake daukar dogon lokaci, kuma dukkan shawarwari da al’ummomi da gwamnatocin kasa da kasa suka yanke, suna da tasiri kan yanayin yaduwar annobar, da lokacin da za a kawo karshen yaduwarta a duniya.

A don haka, yanzu da wahala a iya hasashen yadda yanayin yaduwar cutar tsakanin kasashe zai kasance, saboda bambancin yanayin yaduwar cutar da ma matakin yaki da ita, ganin yadda a wasu kasashe, adadin masu kamuwa da ma wadanda ke mutuwa sanadiyar cutar ke ci gaba da karuwa cikin sauri, yayin da a wasu kuma, ake fuskantar kalubalen sake barkewar cutar. Abu mafi muhimmanci shi ne, ya kamata kasashen duniya su dauki matakan kandagarki bisa halin da suke ciki, a maimaikon dogaro a kan allurar rigakafi kadai. Ba a nan take ba, wai an danne Bodari a ka.

Bincike dai ya nuna cewa, ana fatan a cikin farkon watanni uku na shekarar 2021, za a samar da alluran riga kafin COVID-19 miliyan dari 5 ga kasashe da yankunan dake cikin shirin samar da allurar rigakafin cutar wato COVAX, kana ya zuwa karshen shekarar 2021, za a samar da karin allurar rigakafi a kalla biliyan 2 ga kasashe da yankunan dake cikin wannan shiri.

Amma masu iya magana na cewa, bai kamata da ganin hadari ya yi wanka da najasa ba. (Ibrahim Yaya)