Fasahar sarrafa baka ta kabilar Xibo
2020-12-09 14:49:20 CRI
Malam E Jianye ke nan, dan kabilar Xibo mai shekaru 45 da haihuwa. Malamin yana rayuwa ne a birnin Shenyang na kasar Sin, kuma tun yana shekaru 15 da haihuwa, ya fara bin kakansa koyon fasahar sarrafa baka irin na gargajiyar ‘yan kabilar. Ya ce, a kan shafe sama da shekara guda kafin a hada baka mai inganci. Sai saboda ci gaban zamaninmu, ba a amfani da baka sosai, duk da haka, malamin bai yi watsi da fasahar ba. Bayan aiki, ya kan shirya gasar harbin kibiyoyi, don yayata fasahar. (Lubabatu)