logo

HAUSA

Farfadowar cinikin waje na kasar Sin ya bullo da wasu alamu uku

2020-12-07 21:22:54 CRI

Farfadowar cinikin waje na kasar Sin ya bullo da wasu alamu uku

A watan Nuwambar shekarar da muke ciki, cinikin waje da kasar Sin ta yi ya ci gaba da samun farfadowa sosai. Alkaluman kididdigar da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, bisa farashin dalar Amurka, yawan kudin shige da fice na cinikin wajen kasar Sin ya kai dala biliyan 460.72 a watan Nuwamba, adadin da ya karu da kaso 13.6. Kuma a cikinsu, yawan kudin hajojin fitarwa ya karu da kaso 21.1, sai kuma yawan kudin hajojin da ake shigo da su ya karu da kaso 4.5.

Farfadowar cinikin waje na kasar Sin ya bullo da wasu alamu uku

Farfadowar harkokin cinikin wajen kasar Sin yana samar da babban karfi ga tabbatar da bunkasar sana’o’i a duk fadin duniya. Daga watan Janairu zuwa Nuwambar bana, harkokin shige da ficen da kasar Sin ta yi tare da kungiyar ASEAN, da tarayyar Turai, da Amurka, da Japan da kuma Koriya ta Kudu duk sun samun karuwa ainun.

Farfadowar cinikin waje, da saurin bunkasar masana’antu, da farfadowar kasuwanni, gami da samar da guraban ayyukan yi ga jama’a, duk sun shaida cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana samun murmurewa kuma cikin sauri.

Farfadowar cinikin waje na kasar Sin ya bullo da wasu alamu uku

A saboda haka, akwai kungiyoyin kasa da kasa da dama wadanda suka yi hasashen cewa, Sin za ta kasance babbar kasa daya kadai a duniya, wadda za ta samu karuwar tattalin arziki a bana. Haka kuma kwanan nan, kwamitin manyan jami’an kula da harkokin kudi na duniya na kafar CNBC ta Amurka, ko kuma Consumer News and Business Channel a turance, ya bullo da wani rahoton dake nuna cewa, manyan jami’an kula da harkokin kudi daga wasu manyan kamfanonin kasa da kasa suna ganin cewa, kasar Sin tana bakin kokarinta wajen ganin bayan annobar COVID-19, har ma kuma tattalin arzikinta ya samu habaka sosai.

Duk da cewa ana fuskantar matsalar rashin sanin tabbas, amma ana ganewa ido yadda cinikin waje, gami da tattalin arziki na kasar Sin suke samun farfadowa cikin sauri. Kana, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen waje, da neman ci gaba tare da sauran kasashe, da kuma kokarin tabbatar da bunkasar kasuwanci da tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)