logo

HAUSA

Sin da Rasha za su kara karfafa hadin gwiwa wajen binciken sararin samaniya

2020-12-07 11:06:13 CRI

Sin da Rasha za su kara karfafa hadin gwiwa wajen binciken sararin samaniya

A kwanakin baya an fitar da “hadadden rahoton ganawar firayin ministocin kasashen Sin da Rasha karo na 25”, inda aka bayyana cewa, nan gaba kasashen biyu za su gudanar da hadin gwiwa mai dorewa a tsakaninsu a fannin shawagin tauraron dan-Adam, za kuma su ingiza hadin gwiwar moriyar juna wajen gina tashar binciken duniyar wata ta kasa da kasa, masanan da abin ya shafa sun bayyana cewa, sassan biyu za su ci gajiyar hadin gwiwar dake tsakanin su.

Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Rasha a bangaren bincikin sararin samaniya ya hada binciken duniyar wata, da bincikin sararin samaniya mai nisa, da samar da sinadarin musamman da ake bukata yayin gudanar da aikin nazarin sararin samaniya, da kafa tsarin tauraron dan- Adam, da sarrafa na’urar binciken sararin samaniya daga doron duniya, da binciken kayayyakin dake sararin samaniya da sauransu, bisa hadadden rahoton da aka fitar a kwanakin baya, Sin da Rasha za su kara kyautata ingancin tsarin ba da hidimar shawagi na BeiDou na kasar Sin da GLONASS na kasar Rasha, kuma Sin za ta gina tashar binciken tsarin shawagin GLONASS a kasarta, Rasha ita ma za ta gina tashar binciken tsarin shawagin BeiDou a kasarta, kana kasashen biyu za su gudanar da hadin gwiwa a bangaren sufurin iyakokin kasashensu, da aikin gona na gwaji dake tsakaninsu.

Mataimakin shugaban kwamitin sufurin sararin samaniya na kungiyar zirga-zirgar kasa da kasa, sheihun malamin cibiyar nazari ta biyu ta rukunin kimiyya da masana’antu na zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin, Yang Yuguang ya gayawa wakilinmu cewa, hadin gwiwar dake tsakanin tsarin shawagin tauraron dan- Adam ya dace da sabbin bukatun da ake da su a halin da ake ciki yanzu, saboda hakan zai kyautata hidimar da ake samarwa masu bukata a fadin duniya, yana mai cewa, “A halin da ake ciki yanzu, muhimman tsare-tsaren shawagin tauraron dan- Adam na kasashen duniya suna amfani ne da fasahohi masu kama da juna, lamarin da ya sa karin adadin tauraron bil Adama da ake amfani da su yayin shawagi zai kyautata hidimar, a don haka hadin gwiwar dake tsakanin tsare-tsaren shawagin tauraron dan- Adam yana da muhimmanci matuka.”

Yang Yuguang yana ganin cewa, gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Rasha a bangaren shawagin tauraron dan-Adam, zai amfanin sassan biyu duka, yanzu haka idan Sin ta gina tashar binciken tsarin shawagin GLONASS a kasarta, Rasha ta gina tashar binciken tsarin shawagin BeiDou a kasarta, to hidima da tsare-tsaren shawagin da biyu suke samarwa za ta kara kyautata a bayyane, yana mai cewa, “To ta yaya za a samar da bayanai masu inganci? Ana ganin cewa, ya dace a sarrafa taurarin dan- Adam masu ba da shawagi yadda ya kamata, kuma a gyara su cikin lokaci, kamar yadda aka sani, kasashen Sin da Rasha suna da girma matuka, idan muka iya gyara taurarin dan- Adam na tsarin BeiDou a tashar binciken tsarin da za mu kafa a kasar Rasha, to, mu ma za mu amince da aikin gyara tauraron bil Adama na tsarin GLONASS a kasarmu, hadin gwiwar dake tsakaninmu a bangaren zai amfani sassan biyu duka.”

Kana a bangaren binciken duniyar wata, cibiyar kula da aikin binciken duniyar wata da sararin samaniya ta hukumar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin ta fayyace a kwanan baya cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara zurfafa aikin binciken duniyar wata, wato za ta kara samar da na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6, da Chang’e-7, da kuma Chang’e-8 da sauransu, a sa’i daya kuma, za ta yi hadin gwiwa da sauran kasashe, domin gina tashar nazarin kimiyya da fasaha ta kasa da kasa a duniyar wata.

Bisa hadadden rahoto kan ganawa karo na 25 tsakanin firayin ministocin kasashen Sin da Rasha da aka fitar kwanakin baya, nan gaba kasashen biyu wato Sin da Rasha za su gudanar da hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu wajen gina tashar nazarin kimiyya da fasaha ta kasa da kasa a duniyar wata.

Yang Yuguang yana ganin cewa, hadin gwiwar dake tsakaninsu zata amfani sassan biyu, yana mai cewa, “Fasahar binciken sararin samaniya ta kasar Sin tana da fifiko, saboda tana amfani da fasahohin zamani wadanda ke kan gaba a duniya, Ita kuwa kasar Rasha tana nuna fifiko wajen tattara fasahohin da abin ya shafa.”

Hakazalika, Yang Yuguang ya jaddada cewa, binciken sararin samaniya babban sha’ani ne na daukacin bil Adama, binciken sararin samaniya ta hanyar yin amfani da sararin samaniya cikin lumana shi ne burin daukacin bil Adama/(Jamila)