logo

HAUSA

Gani Ya Kori Ji: Sallar La'asar A Masallacin Kuonaxiehai'er

2020-12-03 16:15:03 CRI

Gani Ya Kori Ji: Sallar La'asar A Masallacin Kuonaxiehai'er

Gani Ya Kori Ji: Sallar La'asar A Masallacin Kuonaxiehai'er

Masallacin Kuonaxiehai'er yana Gundumar Moyu dake yankin Hetian na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta. Masallaci ne da aka gina a shekarar 1905, wato shekaru 115 ke nan. Kasancewarsa babban masallaci mai dogon tarihi ya sa gwamnati ya yi masa-gyare gyare har sau biyu, wato a shekarar 1990 da kuma 2007.

A yanzu haka wannan masallaci na iya daukar masallatai 2000 a lokaci guda.  Masallacin yana da haraba mai fadi, da ban dakunan wanka da na alwala. An kuma samar da dakin karatu mai kunshe da litattafan addinin musulunci daban daban kamar Alqur'ani mai tsarki, da litattafan Hadisi da na fikihu, da na dokoki, har ma da na kimiyya da aka wallafa da Sinanci da kuma yaren al'ummar Uygur.

Yayin ziyararmu wannan masallaci na halarci sallar La'asar tare da musulman wannan wuri. Wannan ya zama shaidar gani da ido dake tabbatar da cewa, musulman wannan yanki suna gudanar da ibadunsu cikin ’yanci.

Bugu da kari, jami'an wannan masallaci sun bayyana min cewa, gwamnati tana samar da dukkanin kudade da kayan aikin kula da wannan masallaci. Baya ga haka, akwai inshorar kula da lafiya ga limamai dake jagorantar masallacin kamar dai irin wadda ake samarwa ga sauran ma’aikata masu gudanar da muhimman ayyukan al'umma.

Muna iya cewa, kafin mutum ya gaskata kafofin dake yada labarun sukar kasar Sin game da harkokin addinai ya dace ya bibiyi rahotanni na ganau dake nuna ainihin halin da wannan yanki na Xinjiang ke ciki.

Kamar yadda Bahaushe kan ce “Gani ya kori Ji” ga wasu hotuna game da ziyara ta wannan masallaci mai tsawon tarihi na Kuonaxiehai'er dake Gundumar Moyu a yankin Hetian na jihar Xinjiang. (Saminu Hassan)