logo

HAUSA

Bai dace a ci gaba da siyasantar da batun COVID-19 ba

2020-12-03 19:35:15 CRI

Bai dace a ci gaba da siyasantar da batun COVID-19 ba

Yanzu dai zurfafa binciken kimiya, na kara fito da karin shaidu dake nuna cewa, annobar COVID-19 ta dade da yaduwa a cikin al’umma.

A matsayin kasar da cutar ta fara bulla, ya sa wasu kafofin watsa labarai da ’yan siyasar kasashen yamma zargin kasar Sin ba tare da hujja ba, musamman makiya kasar ta Sin. Koda yake, zargin da suke yiwa kasar Sin, zargi ne na son kai da dalilai na biyan bukatun siyasa.

Bai dace a ci gaba da siyasantar da batun COVID-19 ba

Sai dai wadannan dabi’u sun yi matukar illa, inda suka kara zurfafa kyamar nuna wariya da rashin yarda tsakanin kasar Sin da kasashen yamma. Amma duk tsuntsun da ya janyo ruwa, shi ruwa zai duka.

A ranar 3 ga watan Disamba, yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a duniya, ya kai 64,4447,657, yayin da cutar ta halaka mutane 1,491,559. A cewar jami’ar John Hopkins, lokaci ya yi da za a kawar da duk wasu bambance-bambancen siyasa da ra’ayi, da rashin fahimta, a kuma yi aiki tare don yakar wannan annoba, ta yadda za a kare rayuka da lafiyar daukacin bil-Adama. (Ibrahim Yaya)