logo

HAUSA

Tattalin arzikin zamani na kasar Sin yana kara habaka

2020-11-30 16:26:08 CRI

Tattalin arzikin zamani na kasar Sin yana kara habaka

Masu hikimar magana na cewa, “sai da ruwan ciki ake jan na rijiya”. Batun tattalin arziki wani muhimmin jigo ne na ci gaban kowace irin al’umma duba da muhimmancin da fannin ke da shi wanda ya kasance tamkar gishiri wanda masu azancin magana ke cewa, “in babu kai ba miya”. Bisa lura da girman alfanu da fa’idojin dake tattare da wannan fannin na tattalin arziki, ya sa gwamnatin Sin ke kara jan damara wajen bullo da sabbin dabaru iri daban daban domin bunkasa fannin. Wani batu mai muhimmanci shi ne, yadda mahukuntan kasar suke bayar da fifiko mai yawa ta hanyar ware makudan kudaden raya tattalin arzikin kasar.

Bayan da duniya ke fama da juyin juya hali ta fannin ci gaban zamani, da halin rashin tabbas da duniyar ke fuskanta, hakan ya sa kasar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen bijiro da hanyoyi daban daban don raya tattalin arzikinta na zamani bisa dacewa da yanayin al’ummarta da kuma bukatun da ake da shi a kasuwannin duniya. Koda a kwanakin baya, sai da cibiyar nazarin fasahar intanet ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto wanda ya nuna cewa, tattalin arzikin zamani na kasar ya yi matukar bunkasa inda ya kai RMB Yuan triliyan 35.8, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 5.45 a shekarar 2019, wanda ya kai kashi 36.2 bisa 100 na yawan GDPn kasar baki daya. Rahoton wanda aka bayyana a lokacin taron dandalin bunkasa fasahar intanet ta duniya, wanda aka gabatar a makon jiya a birnin Wuzhen na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, rahoton ya nuna cewa, barkewar annobar COVID-19 ta kara fito da muhimmancin intanet a fili, yayin da tattalin arzikin zamani ya kasance wani muhimmin ginshiki mai karfi wajen rage tasirin illar annobar ta COVID-19 wacce ta zamewa duniya babbar damuwa, musamman ta fannin daidaita yanayin tattalin arziki da kuma inganta tsarin tafiyar da shugabanci a duniya. Ya zuwa karshen watan Mayu, kamfanin yanar gizo na fiber-optic na kasar Sin ya yi nasarar hadewa dukkan yankunan biranen kasar da na karkara, inda aka samu masu mu’amala da kamfanin na fiber-optic sun kai kashi 93.1 bisa 100 na yawan adadin masu amfani da hanyoyin intanet a duk fadin kasar, wanda kuma shi ne adadi mafi yawa a duk duniya baki daya. Kididdiga ta nuna cewa, hada hadar ciniki na zamani na kasar Sin ya kai yuan triliyan 34.81 a bara, inda aka samu karin kashi 6.7 bisa 100 idan an kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2018. Ko shakka, matakan da shugabannin Sin ke dauka sun taimaka wajen cimma wadannan manyan nasarorin bunkasa fannin tattalin arzikin zamani na kasar. (Ahmad Fagam)