logo

HAUSA

Cibiyar hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kare muhalli za ta amfanawa dukkan bangarorin biyu

2020-11-29 17:22:27 CRI

Cibiyar hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kare muhalli za ta amfanawa dukkan bangarorin biyu

Kwanan nan ne aka kaddamar da cibiyar hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin kare muhalli a birnin Beijing, muhimmin mataki ne da aka dauka domin biyan bukatun al’ummun bangarorin biyu na samun ingantaccen muhallin halittu da kyautata jin dadin rayuwa.

In ba’a manta ba, a wajen taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin-gwiwar Sin da Afirka ko kuma taron FOCAC a takaice, wanda aka yi a shekara ta 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da wasu muhimman shawarwari dangane da kara gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka, ciki har da fannin kiyaye muhallin halittu.

A cewar shugaba Xi, kasarsa na fatan himmatuwa tare da kasashen Afirka, domin kiyaye muhallin halittu, da yin kira ga al’ummunsu su yi rayuwa da raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Har wa yau, ya kamata bangarorin biyu su fadada hadin-gwiwa da mu’amala a fannonin da suka shafi tinkarar sauyin yanayi, da amfani da makamashi mai tsafta, da hana kwararar hamada da zaizayar kasa, tare kuma da kare namun daji da tsirrai wadanda ke fuskantar hadarin bacewa daga doron kasa, ta yadda al’ummun Sin da Afirka za su rayu cikin jin dadi da annashuwa a wannan duniya tamu.

Cibiyar hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kare muhalli za ta amfanawa dukkan bangarorin biyu

Kafa cibiyar hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kare muhalli, daya ne daga cikin alkawurran da gwamnatin kasar Sin ta yi a wajen taron FOCAC, abin da zai taimaka sosai ga samar da dauwamammen ci gaba ga dukkan bangarorin biyu. Gwamnatin kasar Sin ta dade tana maida hankali kan kiyaye muhallin halittu, wato tattalin arzikinta ya bunkasa cikin sauri, amma ba tare da gurbata muhalli ba. Gwamnati tana daukar wasu muhimman matakai a wannan fanni, ciki har da tantance shara bisa dacewa, da kyautata ingancin ruwan koguna daban-daban, da kara dasa bishiyoyi domin hana kwararar hamada, da takaita yawan iska mai gurbata muhallin da ake fitarwa, musamman a wasu masana’antu.

Kasashen Afirka na fuskantar barazana a fannin kiyaye muhallin halittu, ciki har da bala’in fari, da zabtarewar kasa, da yawan sare bishiyoyi da farautar namun daji da sauransu. Najeriya, Allah ya hore mata dimbin albarkatun kasa, musamman man fetur, amma a wasu lokuta, malalar albarkatun mai yana janyo babbar matsalar gurbatar muhalli, da illata rayuwa da lafiyar dan Adam. Don haka, ya dace Sin da Afrika su kara mu’amala da tuntubar juna a fannin kare muhalli, da amfani da wannan dandali na hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kare muhalli, domin lalibo sabbin hanyoyin samar da ci gaba mai dorewa, ta yadda al’ummunsu za su ci gajiyar irin wannan hadin-gwiwa yadda ya kamata. (Murtala Zhang)