logo

HAUSA

Shawarwarin Sin za su ingiza huldar Sin da ASEAN

2020-11-27 19:56:11 CRI

Shawarwarin Sin za su ingiza huldar Sin da ASEAN

A yau Jumma’a 27 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da jawabi ta kafar bidiyo a yayin bikin baje koli na Sin da ASEAN karo na 17, da taron kolin kasuwanci da zuba jari na Sin da ASEAN, inda ya jaddada cewa, ya kamata a gina kyakkyawar makomar Sin da ASEAN, kuma ya gabatar da shawarwari guda hudu, lamarin da ya nuna kudurin Sin na ingiza hadin gwiwar dake tsakaninta da kungiyar ASEAN da kudurinta na ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba yadda ya kamata.

A halin yanzu, tattalin arzikin duniya ya gamu da matsala sakamakon yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, amma wasu hukumomin kasa da kasa da abin ya shafa sun yi hasashen cewa, kila yankin gabashin Asiya zai kasance yanki daya kacal wanda zai samu ci gaban tattalin arziki a fadin duniya, a bisa irin wannan yanayi, kasar Sin ta shirya bikin baje koli na Sin da ASEAN karo na 17, da taron kolin kasuwanci da zuba jari na Sin da ASEAN, kamar yadda aka tsara, lamarin da ya nuna kudurin kasar na nacewa kan manufar bude kofa ga kertare, da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kungiyar ASEAN.

To, ta yaya za a gina kyakkyawar makomar Sin da ASEAN a sabon yanayin da ake ciki yanzu? Kan wannan batu, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari guda hudu, kara karfafa aminci ga juna domin tsara tsarin raya kasashen yankin, kara gudanar da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu domin hanzartar farfadowar tattalin arziki daga duk fannoni a yankin, kara sa kaimi kan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha domin zurfafa hadin gwiwar tattalin arzikin zamani dake tsakanin sassan biyu, kara mai da hankali kan hadin gwiwa wajen kandagarkin annobar COVID-19 domin kara karfin kiwon lafiyar jama’a a yankin.

An lura cewa, bana shekaru goma ke nan da kammala gina yankin cinikayya maras shinge na Sin da ASEAN, an kuma daddale yarjejeniyar huldar tattalin arziki ta sada zumunta daga duk fannoni a yankin a kwanakin baya, duk wadannan za su taimaka wajen zurfafuwar hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.

Ana sa ran cewa, kasar Sin za ta samar da karin damammaki ga kasashen yankin gabashin Asiya ta hanyar shirya bikin baje koli na Sin da ASEAN da taron kolin kasuwanci da zuba jari, ta yadda za ta ba da gudummawa wajen farfafowar tattalin arziki a yankin da kuma ci gaban tattalin arikin duniya baki daya.(Jamila)