logo

HAUSA

Ma’anar bikin yabawa ma'aikacin da ya zama abun koyi a kasar Sin

2020-11-27 14:53:50 CRI

Ma’anar bikin yabawa ma'aikacin da ya zama abun koyi a kasar Sin

Kwanan baya, kasar Sin ta gudanar da gaggarumin bikin yabawa ma’aikacin da ya zama abun koyi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Yayin bikin, shugaban kasar Sin ya ingiza al’ummar Sinawa da su yi koyi da ruhin ma’aikacin da ya zama abun koyi, to ko mene ne ma’anar gudanar da irin wannan biki?

Kowa ya sani, cikakken sunan kasar Sin shi ne jamhuriyar jama’ar kasa Sin, hakan ya sa kasar ta mai da jama’a a gaban komai, saboda jama’a su ne ginshikin al’umma, kuma suke ba da gudummawar bunkasa kasar, kuma su ne masu raya kasar. Wannan ma’aikata da suka zama abun koyi, daya ne daga cikin nagartattun jama’ar kasar. Nuna yabo gare su ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan harkokin jama’arta, kuma za ta karfafa musu gwiwar kara himma da gwazo, wajen raya kasar cikin hadin kai.

Shekarar bara, cutar COVID-19 ta barka ba zato ba tsamani, kuma jama’ar kasar Sin ta nuna goyon baya matuka ga gwamnatin kasar Sin wajen yaka da kandagarkin cutar, daga cikinsu akwai wasu ma’aikata da suka dukufa wajen aiki, har su yi asarar ayyukansu. Idan ba domin sadaukarwar wadannan mutane ba, da Sin ba za ta cimma nasarar hana yaduwar wannan cuta cikin lokaci ba.

Ban da wannan kuma, a wannan shekara, kasar Sin ta cimma nasarar kawar da matsakaicin talauci a duk fadin duniya. Wannan gaggarumar nasara ce ta dogaro da kokarin da ma’aikata dake sassan daban-daban na kasar Sin, Sinawa na matukar son taimakawa juna, da samun wadata cikin hadin kai, bisa ruhin ma’aikacin dake zama abun koyi ga saura.

Bunkasuwar kasar na bukatar gudummawar daidaikun mutane, wadannan ma’aikata da suke zama abun koyi, za su baiwa sauran jama’a nagartattun abubuwa na koyi, don kara ba da gudunmawarsu wajen raya kasar Sin cikin hadin kai, kuma bunkasuwar kasar za ta amfani duk fadin jama’ar kasar, har ma ta samar da wadata tare, ta hakan Sin za ta ba da gudunmawa wajen bunkasuwar duniya gwargwadon karfinta. (Amina Xu)