logo

HAUSA

Dabarun Sin za su ba da jagora wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa bayan ganin bayan COVID-19

2020-11-22 20:19:48 CRI

Dabarun Sin za su ba da jagora wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa bayan ganin bayan COVID-19

A yammacin jiya Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli a matakin farko karo na 15 na shugabannin kasashen G20 ta kafar bidiyo a nan birnin Beijing tare da gabatar da muhimmin jawabi, inda ya jaddada cewa, ya dace a nace kan ka’idar tattaunawa tare da ginawa tare da morewa tare, da ka’idar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, da ka’idar bude kofa ga ketare tare kuma da yin hakuri da juna, da ka’idar gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa domin samun moriya tare, hakika dabarun da ya gabatar za su ba da jagora wajen gudanar da harkokin kasa da kasa bayan ganin bayan annobar cutar numfashi ta CPOVID-19.

Idan an waiwayi tarihin tattalin arziki da cinikayya, za a gane cewa, cudanya za ta ingiza ci gaban tare, rufe kofa zai janyo koma baya, ya zama wajibi a dauki matakan da suka dace bisa hakikanin yanayin da ake ciki, dabarun da shugaban kasar Sin ya gabatar sun nuna matsaya daya da zaman takewar al’ummar kasashen duniya suka cimma.

Kafin shekaru 12 da suka gabata, an kafa tsarin ganawar shugabannin kasashe mambobin G20 ne sakamakon rikicin hada-hadar kudin da ya shafi daukacin kasashen duniya, a cikin wadannan shekaru 12, wannan tsari ya sauya zuwa wani muhimmin dandalin tafiyar da harkokin kasa da kasa, yanzu haka ana fama da matsalar yaduwar annobar COVID-19, ya kamata kasashen G20 su kara taka rawar gani domin warware matsalar, tare kuma da kawo alheri ga al’ummar duniya.

A karkashin yanayin, shugaba Xi ya gabatar da ra’ayoyi guda hudu, wato kara karfafa tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD, da kyautata tsarin habakar tattalin arzikin duniya, da ingiza ci gaban tattalin arzikin zamani, da kuma daga matsayin dakile kalubalolin duniya, ra’ayoyin za su ba da jagora wajen gudanar da harkokin kasa da kasa bayan ganin bayan annobar.

Yanzu ana fama da bazuwar cutar COVID-19, wasu kasashe suna yada “kwayar cutar siyasa”, tare kuma da nuna tababa game da amfanin MDD, duk wadannan sun jefa kasashen duniya cikin mawuyacin yanayi, a don haka shugaba Xi ya jaddada cewa, akwai bukatar kiyaye kwarjini da matsayin MDD da tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, a sa’i daya kuma, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin tattaunawa da sauran kasashen duniya domin fitar da dabarun daidaita matsalolin dake shafar fasahohin zamani.

A bayyane an lura cewa, kasar Sin wadda ke kokarin shimfida zaman lafiya a fadin duniya da ingiza ci gaban duniya da kuma kiyaye tsarin kasa da kasa za ta ci gaba da sanya kokari tare da sauran kasashen duniya domin kara kyautata tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa.(Jamila)