logo

HAUSA

Gudummawar Da Ake Bayarwa Wajen Kare Kayayyakin Tarihi A Yanzu, Za Ta Tallafawa Jika Da Jikokinmu

2020-11-21 16:26:59 CRI

Gudummawar Da Ake Bayarwa Wajen Kare Kayayyakin Tarihi A Yanzu, Za Ta Tallafawa Jika Da Jikokinmu

Kwanakin baya, hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin da gwamnatin birnin Shanghai sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa ta yin kwaskwarima kan ayyukan kula da kayayyakin tarihi na kasa. Cikin yarjejeniyar, an ce, cikin shekaru uku masu zuwa, birnin Shanghai zai fara yin kwaskwarima kan manufofin kula da kayayyakin tarihi, da inganta tsarin kare kayayyakin tarihi, da habaka hanyoyin gudanar da ayyuka da kuma hanyoyin ba da hidima a wannan fanni da dai sauransu, domin neman sabbin hanyoyin karewa da kuma amfani da kayayyakin tarihi.

Kayayyakin tarihi na tuna mana al’adu da tarihin wata kasa, su ne abubuwa mafi muhimmanci da muka gada daga kaka da kakanni, dukkanin gudummawar da ake bayar a halin yanzu wajen kare kayayyakin tahiri, za su iya tallafawa jika da jikokinmu. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, “ba bayyana harkokin tarihi kawai kayayyakin tahiri suke yi ba, suna ba da muhimmin tasiri ga al’ummomi da makomarmu. Suna da daraja gare mu, da ma dukkanin jika da jikokinmu. Shi ya sa, kula da kayayyakin tarihi yadda ya kamata muhimmin nauyi ne dake wuyanmu.”

Kare kayayyakin tarihi yana da amfani wajen karfafa amincewar al’ummomi kan al’adun kasarsu. Idan muka duba wannan batu daga fannin tarihi, za a gane cewa, kare kayayyakin tarihi shi ne kare tarihi da ci gaban al’adu, akwai abubuwa masu yawa da za mu iya koyo daga tarihi. Haka kuma, kare kayayyakin tarihi zai iya karfafa ra’ayin al’umma na kishin kasa, ta yadda zai inganta harkokin yada al’adu da farfadowar kasa bai daya. Sa’an nan, kare kayayyakin tarihi zai iya ba da taimako wajen raya ayyukan yawon shakatawa da karfafa mu’amalar dake tsakanin jama’ar kasa da kasa, lamarin da zai ba da gudummawa wajen inganta bunkasuwar tattalin arziki. Shi ya sa, karfafa ayyukan kare kayayyakin tarihi zai iya tallafawa al’ummomi daga fannoni daban daban. (Maryam Yang)