logo

HAUSA

Kada a bar wata kasa a baya yayin gina kyakkyawar makomar bil adama

2020-11-20 14:39:23 CRI

Kada a bar wata kasa a baya yayin gina kyakkyawar makomar bil adama

A jiya Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shawarwarin shugabannin masana’antu da cinikayya na kungiyar APEC ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi, inda ya jaddada cewa, akwai bukatar kasashen duniya su taimakawa juna yayin da suke cikin mawuyacin hali, su rungumi akidar hadin gwiwa, da karfafa munafar tuntubar juna, ta yadda za su samu dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya da zai kunshi kowa da kowa, da kuma cimma burin gina kyakkyawar makomar bil Adama yadda ya kamata.

An lura cewa, sau da dama shugaba Xi yana nanata bukatar gina kyakkyawar makomar bil Adama, saboda burin yana da matukar muhimmanci ga daukacin kasashen duniya, dalilin da ya sa haka shi ne, makomar kasa da kasa wadanda ke da moriya iri daya ta dogara da juna, ba zai yiyu a raba moriyarsu ba, dole ne su hada kai su yi kokari tare domin samun ci gaba da wadata.

Yanzu haka annobar cutar COVID-19 dake bazuwa a fadin duniya ta sake shaida cewa, bil Adama suna da makoma ta bai daya, babu sauran zabin dake gabansu, ya zama wajibi kasa da kasa su gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu, domin warware kalubalolin duniya.

Hakika kasar Sin ta rika sauke nauyin dake wuyanta yayin da take kokarin taka rawarta wajen gina kyakkyawar makomar bil Adama, misali a gun cikakken taro na biyar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na 19 da aka kira a kwanakin baya, an zartas da shawarar tsara shirin raya kasa bisa shekaru biyar-biyar na 14, inda aka bayyana cewa, kasar Sin za ta tsara sabon tsarin raya kasa ta hanyar yin la’akari da hakikanin yanayin da take ciki, da habakar tattalin arzikin duniya, da kuma sauye-sauyen muhallin kasa da kasa, wato za ta kara mai da hankali kan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, domin sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arziki a kasar, kuma za ta ci gaba da zurfafa kwaskwarimar tattalin arziki, domin ingiza kuzarin kasuwa, kana za ta kara bude kofa ga ketare, domin more damammakin ci gaba tare da sauran kasashen duniya.

Hakazalika, kasar Sin ba ta taba mantawa da ’yan uwanta na kasashen Afirka ba, a ko da yaushe tana kokarin gudanar da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu wato Sin da Afirka bisa dandalin FOCAC, kuma ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda za ta samu ci gaba tare da su, ana sa ran cewa, za a cimma burin gina kyakkyawar makomar bil Adama a fadin duniya yadda ya kamata, ba tare da barin wata kasa a baya ba, musammam kasashen Afirka, saboda daukacin bil Adama suna zaman rayuwa ne a kan duniya guda daya. (Jamila Zhou)

Jamila